Washegarin Biki, Ango da 'Yan Biki 5 Sun Sheka Lahira, Wasu Suna Asibiti Rai a Hannun Allah

Washegarin Biki, Ango da 'Yan Biki 5 Sun Sheka Lahira, Wasu Suna Asibiti Rai a Hannun Allah

  • Ango da wasu 'yan biki biyar sun ce ga garinku washegarin da suka sha shagalin aurensa a kauyen Akutara dake Enugu
  • Kamar yadda aka gano, 'yan bikin sun koma gida amma basu tashi da safe ba sai balle kofa aka yi aka ga gawawwakinsu
  • Har yanzu ba a gano dalilin mutuwar ba amma wasu daga cikin 'yan bikin suna asibiti yayin da 'yan sanda ke bincike

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Enugu - A kalla mutane shida ne suka sheka barzahu bayan sun halarci wani biki a kauyen Akutara dake yankin Adani a karamar hukumar Uzo-Uwani ta jihar Enugu a kwanakin karshen makon nan.

Vanguard ta rahoto cewa, an gano cewa, an kwantar da wasu a asibiti bayan halartar bikin gargajiya a Obollor-Eke dake karamar hukumar Udenu.

Daya daga cikin wadanda lamarin ya ritsa da su mai suna Obinna Dike mai shekaru 31 shi ne angon, wanda jama'a suka halarci bikinsa, jaridar The Nation ta rahoto.

Kara karanta wannan

Karfin hali: An kama wani sojan bogi da ke yiwa mata fashi da makami

Kamar yadda kakakin rundunar 'yan sandan Enugu, Daniel Ndukwe ya bayyana, Dike ya halarci bikin da 'yan uwa da abokan arziki a ranar Juma'a.

Dukkansu sun koma gida Adani kuma suka cigaba da shagalin murnarsu.

"Sai dai, washegari da safe babu wanda ya fito daga dakin da suka kwana, lamarin da yasa aka balle kofar inda aka samesu kwance kumfa na fita daga bakunansu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Da gaggawa aka mika su asibiti inda aka tabbatar da mutuwar shida daga ciki kuma aka ajiye gawawwakinsu don binciken abinda ya kashe shi yayin da sauran ake kula da su," takardar tace.

Kwamishinan 'yan sandan jihar Enugu, Ahmed Ammani ya umarci sashin binciken manyan laifuka na CID da su kaddamar da bincike na musamman domin gano sarkakiyar dake tattare da lamarin.

A yayin ta'aziyya ga iyalan mamatan, kwamishinan 'yan sandan yayi kira ga jama'a da su kwantar da hankansu tare da bada duk wani bayani mai muhimmanci ga 'yan sanda yayin bincike.

Kara karanta wannan

Kyawawan Hotunan Daurin Auren Wasu Yan Najeriya A Dubai Ya Yadu, Sun Yi Shaglin Bikinsu A Saukake

Matashi Mai Shekaru 25 ya Make Matar Babansa da Tabarya, Ya Bayyana Dalilinsa

A wani labari na daban, rundunar 'yan sandan jihar Katsina a ranar Alhamis tace ta kama matashi mai shekaru 25 mai suna Najib Shehu wanda yayi amfani da tabarya wurin halaka matar babansa.

Kamar yadda rundunar 'yan sandan tace, lamarin ya faru a ranar Alhamis da ta gabata kuma a kowanne lokaci za a iya gurfanar da shi a gaban kotu.

Kakakin rundunar, SP Gambo Isah, ya bayyana hakan jim kadan bayan kama Shehu a hedkwatar rundunar a Katsina. An bayyana shi tare da tabaryar da yayi amfani da ita wurin halaka matar mai shekaru 60.

Asali: Legit.ng

Online view pixel