World Cup: Jerin Garuruwa 16 da za ayi amfani da su wajen gasar kofin Duniya a 2026

World Cup: Jerin Garuruwa 16 da za ayi amfani da su wajen gasar kofin Duniya a 2026

  • Gasar cin kofin wasan kwallon kafa na Duniya na shekarar 2026 zai zo da salon da ba a taba gani ba
  • Kasashe uku (Amurka, Kanada da kuma Mexico) suka yi tarayya domin daukar nauyin ‘World Cup’
  • Kasashe 48 za su buga wasannin gasar a tsakanin garuruwa 16 tsakanin New York zuwa Toronto

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

United States - Hukumar kwallon kafa ta Duniya watau FIFA ta bada sanarwar kasashen da za a buga wasan cin kofi na Duniya da za ayi a shekarar 2026.

FIFA ta fitar da jerin Biranen da za a biga wannan gasa ne a wani biki da aka shirya a birnin New York.

A shekarar ta 2026, za a buga gasar Duniyan ne a kasashe uku – Amurka, Kanada da Kanada. Bugu da kari, kasashe 48 ne za su fafata a maimakon 32.

Kara karanta wannan

Mutane 5 sun mutu yayinda aka yi karo tsakanin yan IPOB da wata kungiyar hamayya a Anambra

A Amurka an zabi Biranen Kansas City, Dallas, Atlanta, Houston, New York/New Jersey, Boston, Seattle, Philadelphia, Miami, San Francisco da Los Angeles

Jaridar ESPN ta ce biranen Mexico da aka zaba domin a buga wasanni a gasar sun hada da Guadalajara, Monterrey, da babban birnin kasar, Mexico City.

Kamar yadda mu ka samu labari, Toronto da Vancouver ne kadai Biranen da aka zaba daga Kanada.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Gasar World Cup 2026
Shirin Gasar World Cup 2026 Hoto: www.insidethegames.biz
Asali: UGC

Karon farko a tarihi

Legit.ng Hausa ta fahimci wannan ne karon farko da kasashe uku za su hadu domin dawainiyar gasar cin kofin Duniya wanda ake yi duk bayan shekaru hudu.

A shekarar 2002, kasashen Koriya da Jafan sun yi tarayya wajen shirya wannan gasa. A wancan lokacin Brazil ce ta doke kasar Jamus, ta tafi da kofin zuwa gida.

Idan za a tuna, a 2018 Amurka da makwabanta suka tunkari FIFA domin samun damar daukar nauyin gasar, aka yi dace kasashen suka yi nasara a kan Moroko.

Kara karanta wannan

Aure ya kullu: Bidiyoyi da hotuna daga shagalin bikin Lilin Baba da kyakkyawar amaryarsa Ummi Rahab

Birane 16 da aka zaba

Ga cikakken jerin Biranen nan kamar haka:

1. Atlanta

2. Boston

3. Dallas

4. Guadalajara

5. Houston

6. Kansas City

7. Los Angeles

8. Mexico City

9. Miami

10. Monterrey

11. New York / New Jersey

12. Philadelphia

13. San Francisco Bay Area

14. Seattle

15. Toronto

16. Vancouver

Asali: Legit.ng

Online view pixel