Ondo: PDP Ta Sanya Ranar Fidda Gwani, Daliget 627 Za Su Rabawa Mutum 7 Gardama

Ondo: PDP Ta Sanya Ranar Fidda Gwani, Daliget 627 Za Su Rabawa Mutum 7 Gardama

  • Yayin da ke ta shirye-shiryen gudanar da zaben jihar Ondo, jam'iyyar PDP ta sanar da lokacin da za ta gudanar da na ta zaɓen
  • Jam'iyyar ta sanar da yau Alhamis 25 ga watan Afrilu a matsayin ranar zaben fidda gwaninta a zaben da za a gudanar a watan Nuwamba
  • Akalla daliget 627 ne za su zabi sahihin ɗan takara wanda za su gwabza da sauran jam'iyyu a zaben ranar 16 ga watan Nuwamba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Ondo - Jam'iyyar PDP ta sanar da gudanar da zaben fidda gwani a yau Alhamis 25 ga watan Afrilu a jihar Ondo.

A zaben da za a gudanar a watan Nuwamba, 'yan takarar PDP bakwai ne suka nuna sha'awa a zaben fidda gwanin da za a yi.

Kara karanta wannan

Ondo: Ƙanin tsohon gwamna ya samu tikitin takara, zai gyara jihar a shekara 1

Masu neman tikiti 7 za su fafata a zane fidda gwanin PDP a Ondo
Jami'yyar PDP za ta gudanar da zaben fidda gwani a yau Alhamis a Ondo. Hoto: Sola Ebiseni, Otunba Bamidele Akingboye, Agboola Ajayi.
Asali: Facebook

Daliget nawa za su yi zaben Ondo?

Jam'iyyar PDP ta sanar da cewa akalla daliget 627 za su zaɓi wanda zai yi nasara a zaben fidda gwanin, a cewar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sakataren yada labaran jami'yyar, Kennedy Peretei ya bayyana cewa za a gudanar da zaben karkashin kwamiti mai dauke da mambobi bakwai.

Peretei ya ce kwamitin zai kasance karkashin jagorancin mataimakin gwamnan jihar Bayelsa, Lawrence Ewhrudjakpo, cewar rahoton Vanguard.

An tantance 'yan takara 7 a Ondo

Tuni aka riga aka tantance masu neman tikitin jam'iyyar wanda shugaban kwamitin tantancewa, Sanata Sam Egwu ya jagoranta.

Sanarwar ta ce an zabi 'ya 'yan jam'iyyar watau daliget din ne guda 627 daga kananan hukumomi 18 da ke jihar baki daya.

Za a fara tantance daliget din da misalin karfe 10:00 na safe inda aka shawarci wadanda ba su da alaka da zaben fidda gwanin da su ba da tazara.

Kara karanta wannan

Zaben Ondo: Jigon APC ya hango rashin nasara ga jam'iyya, ya bayyana dalili

Kanin tsohon gwamna ya samu tikitin Ondo

A wani labarin, kun ji cewa dan uwan tsohon gwamnan jihar Ondo, Olusegun Mimiko ya samu nasarar lashe zaben fidda gwani a jihar.

Abass Mimiko ya samu nasarar lashe zaben ne karkashin jam'iyyar ZLP wanda aka gudanar a jiya Laraba 24 ga watan Afrilu.

Ɗan takarar ya nuna godiya ga al'umma tare da yin alkawarin kawo daidaito a jihar cikin shekara daya kacal da hawa karagar mulki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel