Aure ya kullu: Bidiyoyi da hotuna daga shagalin bikin Lilin Baba da kyakkyawar amaryarsa Ummi Rahab

Aure ya kullu: Bidiyoyi da hotuna daga shagalin bikin Lilin Baba da kyakkyawar amaryarsa Ummi Rahab

  • A karshe an kulla aure tsakanin mawaki Lilin Baba da kyakkyawar amaryarda kuma jarumar Kannywood, Ummi Rahab
  • Dubban jama’a sun shaida daurin auren taurarin arewan guda biyu a yau Asabar, 18 ga watan Yuni
  • Tuni hotuna da bidiyon shagalin bikin suka bayyana a shafin soshiyal midiya inda amarya Ummi ta gaji da kyau

Alkawarin Allah ya cika a tsakanin jarumi kuma fitaccen mawaki a masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Shu'aibu Ahmed Idris, wanda aka fi sani da Lilin Baba da kyakkyawar amaryarsa, jaruma Ummi Rahab.

A yau Asabar 18 ga watan Yuni, ne dubban jama’a suka shaida daurin auren manyan jaruman guda biyu.

Amarya da Ango
Aure ya kullu: Bidiyoyi da hotuna daga shagalin bikin Lilin Baba da kyakkyawar amaryarsa Ummi Rahab Hoto: mufeeda_rasheed1/rikadawa1
Asali: Instagram

An yi shagulgula da dama domin raya wannan rana inda amarya Ummi ta fito shar da ita saboda tsabar kyawu da haduwa.

Kara karanta wannan

Mu na tattaunawa da su Peter Obi - Kwankwaso ya tabbatar da shirin taron dangi a 2023

A cikin wani bidiyo da shafin mufeeda_rasheed1 ta wallafa a Instagram, an gano amaryar sanye da fararen tufafi da mayafi tana farin ciki da annashuwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakazalika, Lilin Baba ma ya wallafa wani hadadden bidiyo na amaryar tasa dauke da taken 'Kyakkyawar matata' a shafinsa na Instagram

Ga karin hotuna na bikin a kasa:

Adam Zango ya saki zafafan hotunansa tare da amaryarsa yayin da suka cika shekaru 3 da aure

A wani labarin, mun kawo cewa a ranar Alhamis, 26 ga watan Mayu ne shahararren dan wasan nan na Hausa kuma mawakin zamani, Adam A. Zango ya cika shekaru da auren amaryarsa, Safiya Chalawa.

Adam Zango ya raya wannan rana ta musamman inda ya saki wasu zafafan hotunansa da matar tasa domin murnar wannan tafiya da ta fara mika a rayuwarsu.

Kara karanta wannan

Okowa: Muhimman abubuwa 12 da baku sani ba game da abokin takarar Atiku a PDP

Ana ganin wannan murna tasa ba zai rasa nasaba da yadda suka shafe tsawon shekaru uku ba tare da an ji kansu da amaryar tasa ba sakamakon lakabi da ake masa da mai yawan auri-saki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel