‘Yan Sanda sun yi ram da wanda ya rika sacewa Neymar miliyoyi a akawun bai sani ba

‘Yan Sanda sun yi ram da wanda ya rika sacewa Neymar miliyoyi a akawun bai sani ba

  • ‘Yan Sandan Brazil sun cafke wani mutumi da ake zargin ya shiga asusun mutane ya sace masu kudi
  • Wani ma’aikacin banki ne ake tuhuma da laifin sace Dala 40, 000 daga akawun din ‘Dan wasa Neymar
  • Tauraron bai san an dauki wannan kudi daga akawun dinsa ba, sai daga baya ya sanar da hukuma

Brazil - Jami’an ‘yan sanda na kasar Brazil sun kama wani mutumi da ake zargi ya yi kutse cikin asusun bankin Neymar, ya yi ta sace masa kudi kadan-kadan.

Jaridar Reuters ta rahoto cewa ana zargin wannan mutum ya yi ta daukar kudi, har ya yi gaba da abin da ya kai fam Dala 40, 000 daga asusun ‘dan wasa Neymar Jr.

A wani jawabi da ‘yan sanda suka fitar a Sao Paulo, wannan mai kutse yana aiki ne a wani banki da ba a ambaci sunansa ba, da Neymar da mahaifinsa suke ajiya.

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun yi awon-gaba da Mai jego, jariri da wasu mutane a Kaduna a daren Juma'a

Jawabin da aka fitar a ranar Laraba, 9 ga watan Fubrairu 2022 ya bayyana cewa wannan ma’aikacin banki da aka kama yana da shekaru 20 ne da haihuwa.

Wannan mutumi ya rika daukar kudi marasa yawa ne daga akawun din shahararrun mutanen da suke da dukiya. Neymar yana cikin wadanda tsautsayi ya fada masu.

Neymar
‘Dan wasan gaban PSG, Neymar Jr. Hoto: www.reuters.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ana tunanin cewa mahaifin ‘dan wasan ne yake kula da kudin da suke cikin asusun bankin na sa.

Fabio Pinheiro Lopes

Hukumar NAN ta ce rundunar ‘yan sanda ba ta bayyana sunan wanda aka damfara ba, ta dai ce ana zargin matashin da satar kudin masu yin ajiya a wannan banki.

Jami’in ‘dan sandan, Fabio Pinheiro Lopes ya yi wannan jawabi ne a shirin talabijin na Brasil Urgente, ya ce wadanda aka yi wa satar ba su ankara da farko ba.

Kara karanta wannan

Sokoto: Kansila ya gwangwaje 'yan unguwarsa da kyautar tabarmai 2, ya jawo cece-kuce

“Mutanen nan ba su gane ba. Ya tura reais 10,000 kusan Dala 1,912.59. Sannan ya sake aika wasu 10, 000, daga nan ya kuma tura wasu 20, 000, sai 50, 000.”
“Gaba daya dai kenan ya dauki reais 200, 000. Da suka gane, sai suka tuntubi bankin, kuma aka dawo masu da kudinsu, ake binciken wanda ya aikata."

- Fabio Pinheiro Lopes

'Yan kwallo masu kyauta

Kwanaki kun ji cewa Neymar yana cikin 'yan wasan kwallon kafa da suke rayuwa cikin daula da facaka da dukiya saboda irin albashin da yake karba a Faransa.

Amma duk da haka 'dan kwallon ya na da matukar kyauta da taimakon mutane. A sahun 'yan wasan da ke taimakon al'umma akwai Sadio Mane da Ozil Mesut.

Asali: Legit.ng

Online view pixel