Ronaldo, Ozil, Mane da sauran ‘Yan kwallon kafa da suka fi kowa taimakawa marasa karfi

Ronaldo, Ozil, Mane da sauran ‘Yan kwallon kafa da suka fi kowa taimakawa marasa karfi

  • Baya ga buga kwallon kafa, akwai wasu ‘yan wasan da suka yi suna wajen yin kyauta da alheri
  • Sadio Mane yana cikin wannan jeri saboda yadda yake taimakawa al’ummar kasarsa ta Sanagal
  • Haka zalika akwai Ozil Mesut wanda dubunnan marasa karfi su ke samun abinci a sanadiyyarsa

An san mafi ‘yan wasan kwallon kafa da rayuwa cikin daula da facaka da dukiya saboda irin albashin da suke samu, amma ba duk aka zama daya ba.

A wannan rahoto da muka tsakuro daga Sportszion da Sportmob, mun kawo wasu ‘yan kwallon da suke amfani da dukiyarsu wajen taimakawa al’umma.

Ga jerin na mu nan:

1. Sadio Mane

Wanda muka fara da shi a jerin na mu shi ne Sadio Mane. Kwanaki CNN ta rahoto cewa ‘dan wasan na Liverpool ya bada $693,000 wajen gina asibiti.

Kara karanta wannan

Jerin matsaloli 6 da Kwankwaso yake bukatar ya tsallake kafin ya shiga Aso Rock a 2023

Sadio Mane ya bada wadannan kudi ne domin a gina asibiti a kauyensu na Bambali a Sanagal. Baya ga haka akwai ayyukan alherin da yake yi a kasarsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

2. Ozil Mesut

Tsohon ‘dan wasan Arsenal da Real Madrid, Ozil Mesut ya dade yana taimakawa gajiyayyu da marasa hali, kuma ya kan yi magana idan ya ga ana zalunci.

Bayan ya lashe gasar kofin Duniya, Mesut ya bada kyautar kudin da ya samu domin ayi wa wasu magani. Tauraron ya yi fice wajen dawainiyar marasa lafiya.

Ronaldo, Ozil, Mane dsr
Yan wasa masu kyauta Hoto: www.eurosport.com da sportmob.com
Asali: UGC

3. Lionel Messi

Lionel Messi ya tashi ne a kasar Argentina a halin da babu yabo babu fallasa. Har yanzu bai manta da tushensa, ‘dan wasan yana cikin masu taimakawa mutane.

Gidauniyar Leo Messi Foundation ta na kokari wajen taimakawa marasa karfi da ilmin boko da kula da lafiyarsu, sannan kuma Messi jakada ne na UNICEF.

Kara karanta wannan

Mun shiga uku: Tsadar man fetur ya sa 'yan Najeriya kuka, sunyi zazzafan martani

4. Neymar Jr.

Neymar yana cikin ‘yan kwallon da suka fi kowa albashi a Duniya, sannan kuma yana cikin wadanda suke taimakawa al’umma daidai bakin gwargwado.

Akwai wani kokari da ‘dan wasan na PSG ya sa a gaba watau “Waves for Water” domin samar da ruwan sha ga mutanen Brazil baya ga sauran alherin da yake yi.

5. Cristiano Ronaldo

Rahoton Sport Mob ya nuna Cristiano Ronaldo yana cikin ‘yan kwallon da suka yi fice wajen kyauta, hakan ta sa ya taba lashe kyautar “Athletes Gone Good Award”.

Ronaldo ya taba biyan $83,000 domin ayi wa wani karamin yaro magani. A 2012 ‘dan wasan ya tara kusan Dala miliyan biyu domin a taimakawa mutanen yankin Gaza.

6. Mario Balotelli

Babban abin mamakin wannan jeri shi ne Mario Balotelli wanda aka sani da rashin da’a. Rabin kudin ‘dan wasan su na karewa ne wajen taimakawa ‘Yan Afrika.

Kara karanta wannan

Sheikh Gadon Kaya: An yi min gurguwar fahimta game da batun mata ma'aikatan kiwon lafiya

A jerin na mu akwai ‘yan wasa irinsu Jermain Defoe wanda gidauniyarsa ta Jermain Defoe Foundation ta ke taimakawa Bayin Allah da-dama a kasar Birtaniya.

Haka zalika 'dan wasan tsakiyar nan, Gareth Barry ya na taimakawa wadanda ba su da karfi. A cikin wadanda suka yi ritaya akwai Didier Drogba da Nnwanko Kanu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel