Bayan an yi waje da zakarun 2019, Super Eagles sun san da wa za su hadu a AFCON

Bayan an yi waje da zakarun 2019, Super Eagles sun san da wa za su hadu a AFCON

  • An hada Tunisiya da Najeriya a zagaye na gaba da za a buga a gasar AFCON na wannan shekarar
  • Super Eagles sun saba lallasa Kasar Tunisiya a tarihi, wannan ne zai zama haduwarsu na biyar
  • Za a gwabza tsakanin kasashen Afrikan a ranar Lahadi a babban filin Kamaru na Roumde Adjia

Cameroon - ‘Yan wasan Super Eagles na Najeriya za su goge raini da kasar Tunisiya a zagaye na biyu na gasar cin kofin kwallon kafa na nahiyar Afrika.

Rahotanni sun tabbatar da Najeriya za ta hadu da Tunisiya bayan kasar Arewacin Afrikar ta samu fitowa daga gurbin rukuni, bayan an yi waje da Aljeriya.

Zakarun nahiyar Turai na 2019, Aljeriya sun sha kashi a wasansu na karshe a hannun Ivory Coast da ci 1-3. Haka zalika Gimbia ta doke Tunisiya da ci 1-0.

Kara karanta wannan

Yadda Gwamnatin Buhari ta taimakawa mutane sama da 500, 000 inji Dr. Isa Pantami

A daidai wannan lokaci kuma Najeriya ta kai mataki na gaba bayan ta yi nasara a wasanninta uku. Super Eagles sun doke Masar, Sudan da Guinea Bissau.

Tarihin haduwarsu a baya

Sau hudu Najeriya ta na haduwa da Tunisiya a tarihi, kuma Super Eagles suke samun nasara. A 1978 ne Najeriya ta fara wasa da Tunisiya, kuma ta doke ta.

Super Eagles
Super Eagles v Tunisia Hoto: @SSE_NGA
Asali: Twitter

Tunisiya ta na 1-1 da Najeriya a gasar AFCON 1980, sai ‘yan wasan ta suka fice daga filin kwallo saboda zargin alkalin wasa da rashin adalci wajen yin busa.

Bayan shekaru 26 aka sake hada Najeriya da kasar Tunisiya, a nan ma aka doke Tunisiya a finariti. Bayan nan Super Eagles ta sake samun galaba a kansu.

Super Eagles sun kara da Carthage Eagles a gasar AFCON na shekarar 2019 inda Najeriya ta samu nasara da ci 1-0 ta kafar ‘dan wasan gaba, Odion Ighalo.

Kara karanta wannan

Shirme ne: ‘Yan Twitter da Facebook sun yi kaca-kaca da Dalar shinkafar da aka yi a Abuja

Burkina Faso/Gabon su na jira

Goal.com ta ce ‘yan wasan na Augustine Eguavoen za su fafata da yaran Mondher Kebaier a filin wasan Roumde Adjia da ke garin Garoua, a kasar Kamaru.

Duk wanda ya yi nasara a ranar Lahadi zai hadu da Burkina Faso ko Gabon a mataki na gaba.

Maki 9 a wasanni 3

A makon nan ne ‘Yan wasan Super Eagles su ka doke kasar Guinea Bissau a gasar AFCON da ake bugawa, hakan ya sa kasar ta gama zagayen da maki tara.

Muhammadu Buhari ya fito ya taya ‘Yan wasan Najeriya murna bayan nasarar da suka samu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel