Shirme ne: ‘Yan Twitter da Facebook sun yi kaca-kaca da Dalar shinkafar da aka yi a Abuja

Shirme ne: ‘Yan Twitter da Facebook sun yi kaca-kaca da Dalar shinkafar da aka yi a Abuja

  • A ranar Talata, 18 ga watan Junairu, 2022 aka kaddamar da dalar shinkafa a birnin tarayya Abuja
  • Rahotanni sun ce duk Duniya babu inda aka tara tulin buhunan shinkafa irin wadanda aka gani
  • Masu amfani da dandulan zumunta sun yi tir da wannan tsari, su kace hakan ba zai tsinana komai ba

FCT, Abuja - A cikin makon nan ne Mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da dalar buhunan shinkafar da aka noma a jihohin Najeriya.

Legit.ng Hausa ta bibiyi martanin da mutane suke yi a game da wannan cigaban da aka samu.

Masu amfani da shafukan sada zumunta sun tofa albarkacin bakinsu kan wannan lamari. Amma da-dama sun nunawadannan buhuna ba za su amfani talaka ba.

Mohammed Jammal a shafinsa na Twitter na @WhiteNigerian ya rubuta cewa:

Kara karanta wannan

Matsalar Tsaro: Baicin kwarewar Buhari, da Najeriya ta ruguje kurmus

“Najeriya ta kaddamar da mafi girman dalar shinkafar Duniya a Abuja.”
"A lokacin da ake da dalar gyada a Kano, Kadana su ake yi a nan, ana jiran a fita da su. Menene amfanin dalar shinkafar nan Muhammadu Buhari?" - Farfesa Jibril Ibrahim
Dalar shinkafar da aka yi a Abuja
Dalar shinkafa a Abuja Hoto: shafin @MuhammaduBuhari/Facebook
Asali: Facebook

Da hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmaad ya nuna hotunan tarin buhunan shinkafa, sai Dr. Kabiru Turaki ya maida masa martani, ya ce an bar Najeriya a baya.

Shehu Sani ya yi abin da ya saba, ya tofa albarkacin bakinsa:

"An kaddamar da wayar da aka kera a Najeriya, sai ta bace. Aka kaddamar da mota mai amfani da wutar lantarki ‘yar Najeriya, sai ta bace. Mu na fatan dalar shinkafar Abuja ba za ta bi hanyar motar da wayar ba."

Kara karanta wannan

Karya ne: NEC ba ta kai ga kara kudin man fetur daga N165 zuwa N300 ba - Osinbajo

Pharm. Jamilu Maiwada ya ce:

“Ayi tunanin irin jigilar dakon waannan shinkafa zuwa Abuja saboda wannan soki-burutsu. Duk mun san wannan shinkafar ba daga Abuja ta ke ba. Ko dai da gaske ba Buhari ba ne, Jibril din ne da ake fada daga Sudan?”

Da yake magana a Whatsapp, wani malamin ilmin aiki jarida kuma masu tofa baki a kan al’amurar yau da kullum, Dr. Muhammad Hashim Sulaiman ya ce da sake.

Dr. Hashim Sulaiman ya ce abu mafi takaici shi ne masu yawo da hotunan bogi da sunan dalar.

Shi kuma Dr. Hakeem Baba Ahmed ya rubuta:

“Yanzu shinkafa mai arha sai a zo Abuja kenan ko? Ga dalar buhu miliyan, da aka dauko da miliyoyi, aka kawo garin masu miliyoyi, saboda miliyoyin talakawa masu neman shinkafa arha su kashe miliyoyi su zo su siya. Tirkashi.”

Satar kudi a NPA?

Tsohuwar shugabar hukumar NPA ta kasa, Hadiza Bala Usman ta ce ana neman bata mata suna ne de zargin ta wawuri kudin gwamnati a lokacin da ta ke ofis.

Kara karanta wannan

Alamar tambaya: Garba Shehu ya lallaba ya bibiyi shafin kamfen din Tinubu a Twitter

Hadiza Bala Usman ta ce a kawo hujjar da ke nuna ta yi sata, a fito ya bayyanawa kowa a Duniya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel