AFCON: Duk da ya na jirgi a hanyar dawowa daga Gambia, Buhari ya tuna da Super Eagles

AFCON: Duk da ya na jirgi a hanyar dawowa daga Gambia, Buhari ya tuna da Super Eagles

  • ‘Yan Super Eagles sun doke kasar Guinea Bissau a gasar AFCON da ake bugawa a kasar Kamaru
  • Muhammadu Buhari ya fito ya taya ‘Yan wasan Najeriya murna bayan nasarar da suka samu a jiya
  • Shugaban kasar ya yi kira ga tawagar Super Eagles su cigaba da wannan kokari, har su lashe kofin

Cameroon - A ranar Laraba, 19 ga watan Junairu, 2022 ne Najeriya ta buga wasan rukuni na karshe a gasar kofin wasan kwallon kafan nahiyar Afrika.

Mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya tawagar ‘Yan wasan Super Eagles murna a kan irin nasarorin da suke ta samu a gasar na AFCON 2021.

Da yake jawabi a shafin Facebook, Muhammadu Buhari ya taya ‘yan kwallon kafan Najeriya murnar lashe wasanninsu uku da samun zuwa zagaye na gaba.

Kara karanta wannan

Sanatocin jihar Katsina 2 sun yi watanni 25 a Abuja, ba su kawo korafi ko shawara 1 ba

“Ina taya Super Eagles dinmu murnar lashe duka wasanninsu uku, da zuwa zagaye na biyu a gasar AFCON cikin salo.”
“Ina kira a gare su, su cigaba da irin wannan kokari, su ma kara kaimin da suka yi wajen zama jagororin rukuninsu.”
“Kuma su dage wajen zama Jakadan Najeriya a filin kwallon kafa da wajen filin wasa.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Buhari ya tuna da Super Eagles
AFCON: Duk da ya na hanyar dawowa daga kasar Gambia, Buhari ya tuna da Super Eagles
Asali: Facebook

Sai kun ci kofi - Buhari

“Daukacin kasar nan ta na sa ran nasara daga gare ku a wasanni bakwai da za a buga har zuwa karshen gasar.”
“An yi uku, saura hudu.” - Muhammadu Buhari

A karshe shugaban Najeriyan ya ce zai cigaba da ba Super Eagles duk wata goyon baya da gudumuwa.

Masu magana a Facebook

Masu bibiyar shugaban kasar a Facebook irinsu Yakson Wudil suka ce ‘Allah ya ba Najeriya sa’a.”

Kara karanta wannan

EFCC ta na binciken mutum 5 a cikin masu neman hawa kujerar Shugaban jam’iyyar APC

Sai ma mun dauko world cup (kofin Duniya)

- Sabiu Andaza

Super Eagles sun yi matukar kokari.

- Hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmaad

Janar bai samun nasara a yaki sai da taimakon sojojinsa. Udumuwar da ka bada ta taimaka sosai wajen wannan nasara.

- Abubakar Aliyu Ahmed

A hanyar dawowa Najeriya

Legit.ng Hausa ta lura shugaba Muhammadu Buhari ya yi wannan magana ne da kimanin karfe 11:00 na dare bayan an tashi wannan wasa a kasar Kamaru.

A daidai lokacin ne jirgin shugaban kasar yake durowa Kaduna daga kasar Gambia inda Buhari ya halarci bikin rantsar da takawarsa Adama Barrow a Banjul.

Asali: Legit.ng

Online view pixel