Yanzu-yanzu: Kungiyar kwallon kafa ta Everton ta kori manajan ta, Rafael Benitez

Yanzu-yanzu: Kungiyar kwallon kafa ta Everton ta kori manajan ta, Rafael Benitez

Kungiyar wasan kwallon kafa ta Everton ta fatattaki manajan ta Rafael Benitez a ranar Lahadi, bayan wata takwas da ya karba ragamar kungiyar.

An nada Benitez matsayin a watan Yuni na shekarar da ta gabata, Daily Trust ta ruwaito.

Yanzu-yanzu: Kungiyar kwallon kafa ta Everton ta kori manajan ta, Rafael Benitez
Yanzu-yanzu: Kungiyar kwallon kafa ta Everton ta kori manajan ta, Rafael Benitez. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Dan asalin kasar Spain din ya fuskanci wannan hukunci ne bayan lallasa su sau tara da aka yi a wasanni 13 inda aka rufa da ci biyu da daya wanda Norwich ta yi musu a ranar Asabar da ta gabata.

"Kungiyar kwallon kafa ta Everton ta na tabbatar da tafiyar Rafael Benitez a matsayin manajan kungiyar," takardar da kungiyar ta fitar ta ce.
“Benitez, wanda ya fara aiki da kungiyar kwallon kafa ta Everton a 2021, ya kuma bar kungiyar daga yau.

Kara karanta wannan

Ina mata fatan alkhairi, amma mafi alkhairin mutum muke bukata a 2023: Gwamnan Oyo ga Tinubu

"Za a bayar da sanarwa kan wanda zai maye gurbinsa a nan gaba."

Masoyan kungiyar kwallon kafa na Everton sun bayyana bukatarsu ta fatattakar Benitez tun a wasan karshe da aka lallasa su na Norwich, Daily Trust ta ruwaito.

Sun dinga ihun ba sa so kuma sun rike takardu masu inkiyar 'Benitez ya bar kungiyar mu', yayin da wani masoyin kungiyar ya yi yunkurin shiga filin wasan tare da yunkurin nada masa na jaki.

Everton ta yi taron majalisar zartarwa na gaggawa a yammacin Asabar domin tattaunawa kan makomar Benitez, hakan ne yayi sanadin barinsa kungiyar.

Benitez ya fusata masoyan Everton ta yadda ake kwatanta su da 'yan karamar kungiya a yayin da ya ke

A watan da ya gabata, Moshiri ya tsaya wa Benitez, inda ya dinga ikirarin cewa dan shekara sittin da dayan zai samu karin lokaci domin kawo gyara a lamurransu.

Kara karanta wannan

Dalilin da yasa na ki aure tun bayan mutuwar Maryam Babangida, IBB

Ammam kuma sakamakon Everton ya nuna cewa babu wata alama ta cigaba kuma yadda masoyan Everton ke nunawa ya bayyana cewa sai Benitez ya tafi.

Daga ƙarshe, Manchester United ta kori Ole Solskjaer

A wani labari na daban, daga karshe dai kungiyar kwallon kafa na Manchester United ta sallami manajan ta Ole Gunner Solskjaer.

Kungiyar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a shafinta a Instagram a safiyar ranar Lahadi.

Hakan na zuwa ne bayan kayen da United ta sha a hannun Kungiyar Watford a Vicarage Road inda aka lallasa ta 4 - 1.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel