Yanzu-Yanzu: Daga ƙarshe, Manchester United ta kori Ole Solskjaer

Yanzu-Yanzu: Daga ƙarshe, Manchester United ta kori Ole Solskjaer

  • An sallami Ole Gunnar Solskjaer daga aikinsa a kungiyar kwallon kafa ta Manchester United da ke Ingila
  • Kungiyar, cikin sanarwar da ta fitar a safiyar ranar Lahadi 21 ga watan Nuwamba ta ce korarsa ba yi mata dadi ba
  • United ta mika godiyarta ga manajan dan asalin kasar Norway tana mai cewa ba za ta taba mantawa da rawar da ya taka a kungiyar ba

Ingila - Daga karshe dai kungiyar kwallon kafa na Manchester United ta sallami manajan ta Ole Gunner Solskjaer.

Kungiyar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a shafinta a Instagram a safiyar ranar Lahadi.

Hakan na zuwa ne bayan kayen da United ta sha a hannun Kungiyar Watford a Vicarage Road inda aka lallasa ta 4 - 1.

Kara karanta wannan

Daliba a jami'ar Umaru Yar’adua ta sha piya-piya don saurayinta ya rabu da ita, an kaita asibiti

Yanzu-Yanzu: Daga karshe, Machester United ta kori Ole Solskjaer
Daga karshe, Machester United ta kori Ole Solskjaer. Photo: Simon Stacpoole
Asali: Getty Images

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bayan kayen da suka suka sha, shugabannin kungiyar United sun yi wani taro na kimanin awanni biyar inda suka cimma matsayar cewa ya kamata a sallami Solskjaer.

Cikin sanarwar da ta fitar, United ta yi wa kocin mai shekaru 48 godiya tana mai cewa ba za ta taba mantawa da shi ba a tarihinta.

Kungiyar ta fitar da sanarwar ne ta shafinta tana cewa:

"Tarihi ba za ta taba mantawa da Ole ba a Manchester United kuma cikin nadama ne muka yanke wannan shawarar mai wahala.
"Duk da cewa makonni uku da suka shude ba su yi wa kungiyar dadi ba, hakan ba zai sa a manta dukkan kwazon da ya yi ba cikin shekaru uku da suka wuce na gina kungiyar.
"Muna yi wa Ole godiya matuka tare da fatan alheri gare shi bisa abubuwan da zai yi a gaba.

Kara karanta wannan

Kotu tayi fatali da karar da aka shigar a kan kudin Janar Abacha da aka dawo da su a 2020

"Ba za a taba mantawa da matsayinsa a tarihin kungiyar ba, ba ma a matsayin dan wasa ba kadai har a matsayinsa na manaja wanda ya bada gagarumar gudunmawa. Muna maraba da shi a Old Trafford har abada a matsayin dan Manchester."

Kazalika, United ta tabbatar da nadin Michael Carrick a matsayin wanda zai cigaba da kulawa da kungiyar a wasanninsu na gaba a yayin da za ta nemi manajan wucin gada zuwa karshen kakar wasan.

Matashin ‘Dan wasa mai shekara 23 da ya fi su Messi, Neymar da Cristiano Ronaldo kudi

Ana ganin cewa babu wanda ya sha gaban Lionel Messi da Cristiano Ronaldo a cikin ‘yan kwallon kafa idan ana maganar kwarewa da dukiya.

Sai dai akwai Faiq Bolkiah mai shekara 23 wanda ana tunanin ya dama su, ya shanye a arziki. The Sun tace Bolkiah yana zaman jiran gadon fam biliyan £13.

‘Dan wasan mai bugawa kungiyar Maritimo a kasar Portugal yana cikin wadanda za su gaji Sarkin kasar Brunie, Hassanal Bolkiah, da zarar ya kwanta dama.

Asali: Legit.ng

Online view pixel