Da Dumi-Dumi: Jarumin Kannywood ya musanta rahoton cewa ya mutu

Da Dumi-Dumi: Jarumin Kannywood ya musanta rahoton cewa ya mutu

  • Jarumi Sani Garba SK na masana'antar shirya fina-finan Hausa Kannywood, ya musanta rahoton da ake yaɗawa cewa ya mutu
  • Jarumin yace bai mutu ba yana nan a raye, amma idan lokacinsa ya yi zai mutu domin kowane rai mamaci ne wata rana
  • A makon da ya gabata ne, Rahoton mutuwar shahararren Jarumin mai wasan barkwanci ya karaɗe kafafen sada zumunta

Kano - Jarumin masana'antar shirya fina-finan Hausa Kannywood, Sani Garba, ya musanta jita-jitar da ake yaɗa wa cewa ya mutu a kafafen sada zumunta.

A makon da ya gabata ne akai ta yaɗa jita-jitar cewa shahararren jarumin mai wasan barkwanci ya kwanta dama musamman a kafafen sada zumunta.

Sai dai a wani sakon bidiyo da jarumin ya yi, kuma abokin aikinsa a masana'antar Kannywood Abba Almustapa, ya saki a Instagram, Garba yace yana nan da ransa bai mutu ba.

Read also

Daliba a jami'ar Umaru Yar’adua ta sha piya-piya don saurayinta ya rabu da ita, an kaita asibiti

Sani Garba
Da Dumi-Dumi: Jarumin Kannywood ya musanta rahoton cewa ya mutu Hoto: premiumtimesng.com
Source: UGC

Yace:

"Ga ni kuna gani a gabanku, ban mutu ba ina nan a raye, amma idan lokaci na ya yi zan mutu, ba sai kun yayata cewa na mutu ba."
"Ina nan ban mutu ba amma idan lokacina ya yi dole zan mutu, kuma ina amfani da wannan dama wajen mika godiya ta ga masana'antar Kannywood baki ɗaya bisa ɗawainiya da ni."
"Ina mika godiya ta ga baki ɗaya mutanen dake Kannywood, sun kasance masu taimaka mun da kuɗi da kuma duk abinda ya dace."

Shin jarumin ba shi da lafiya ne?

Jarumin, wanda ke fama da ciwan Suga, ya bayyana cewa yana samun sauki kuma yana cigaba da ganin likita kamar yadda aka umarce shi.

Garba SK na ɗaya daga cikin jaruman Kannywood masu barkwanci, waɗan da suka jima suna fitowa a fina-finai, kuma a wani lokacin ya fitowa ne a matsayin Uba.

Read also

Ni da mahaifiyata muna kallo lokacin da aka zare ran kanina amma babu yadda muka iya - Dangote

A wani labarin kuma Batun Jaruma Rahama Sadau da wasu sabbin muhimman abubuwa 4 da suka faru a Kannywood

A wannan makon an samu wasu muhimman abubuwa guda 5 masu muhimmanci da suka faru a Kannywood.

Daga cininsu shine batun raɗin sunan jaririyar da aka haifa wa Adam Zamgo, da kuma abinda ya shafi Rahama Sadau.

Source: Legit.ng News

Online view pixel