Daliba a jami'ar Umaru Yar’adua ta sha piya-piya don saurayinta ya rabu da ita, an kaita asibiti

Daliba a jami'ar Umaru Yar’adua ta sha piya-piya don saurayinta ya rabu da ita, an kaita asibiti

  • Dalibar makaranta ta yi yunkurin aika kanta barzahi saboda tsinkewar igiyar soyayya tsakaninta da saurayinta
  • Majiyoyi sun bayyana cewa an garzaya da ita asibiti bayan da ta kife sumammiya
  • Hukumomi a jami'ar basu yo tsokaci kan lamarin ba har yanzu

Katsina - Wata dalibar aji uku a jami'ar Umaru Musa Yar’adua, jihar Katsina ta kwankwandi gorar sabulun tsaftacce hannu da piya-piya bayan saurayinta ya rabu da ita.

21st CC ta ruwaito cewa majiyoyi sun bayyana sunan yarinyar matsayin Ummi, kuma yar jihar Kaduna ce amma tana da yan uwa a Katsina.

Wata daliba da ta bukaci a sakaye sunanta tace:

"Da daren nan (Juma'a) shi (saurayin) ya zo dakin kwanan mata ya fadawa Ummi ya rabu da ita. Bamu san ainihin abinda ya hadasu ba, ko wadanda ke daki daya da Ummi basu san takamammen abinda ya hadasu ba."

Kara karanta wannan

Gwamnati ta fara rabawa talakawa kudi N1.6bn a jihar Jigawa

"Sai ta koma daki ta dauki hand sanitizer da pia pia don fushin abinda yayi mata."

Daliba a jami'ar Umaru Yar’adua ta sha piya-piya don saurayinta ya rabu da ita, an kaita asibiti
Daliba a jami'ar Umaru Yar’adua ta sha piya-piya don saurayinta ya rabu da ita, an kaita asibiti
Asali: Facebook

Saurayin wanda sunansa bai bayyana ba har yanzu shima dalibi ne a jami'ar UMYUK ne.

Wata majiyar ta bayyana cewa shan piya-piyan ke da wuya ta fara amai kuma ta sume.

Tace:

"Abokan kwananta sun sanar da jami'ar kai tsaye kuma aka turo motar asibiti don kai ta asibiti."

Asali: Legit.ng

Online view pixel