Albashin ma'aikata
An ji cewa Gwamnatin jihar Jigawa ta sanar da cewa za a biya ma’aikata N10, 000 a rage radadin tsadar fetur. NLC ta ce wannan ya yi kadan a halin da ake ciki.
Ma’aikatan gine-gine sun tafi yajin-aikin kwana 3 daga yau. Kungiyoyi sun ce rayuwa tayi wahala amma an bar su cikin kunci tuni wasu gwamnatoci sun yi karin albashi.
Ma'aikatan tarayya sun fara 'yan guna-guni yayin da gwamnati ta gaza cika alkawarin da ta dauka na yin albashi a ranar Alhamis, kuma ba a biya su naira dubu 35 ba.
Shugaban ƙungiyar NLC na ƙasa, Joe Ajaero, ya bayyana cewa da yawan gwamnonin da aka sa a kwamitin mafi ƙarancin albashi ba su iya biya a jihohinsu.
An bar maganar N30, 000, NLC ta ce ya kamata mafi karancin albashi ya zama $300 ne a wata. 'Yan kwadago ba su yanke wani albashi ba, amma N200, 000 ya yi kadan.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi na’am da kafa kwamiti na musamman da zai duba lamarin yin karin albashi, mun kawo cikakken jerin ‘yan kwamiti.
Gwamnatin tarayya karshin jagorancin shugaba Bola Tinubu ta kaddamar da kwamitin mutane 37 da zai yi aiki don kara mafi karancin albashi na ma'aikatan kasar.
Sanata George Akume ya sanar da za a rantsar da kwamitin karin albashi. Ranar Talata gwamnati za ta kaddamar da kwamitin da zai yi aikin karin albashin ma’aikata
Gwamnatin jihar Kogi karkashin Gwamna Yahaya Bello ta dakatar da biyan albashin ma'aikata 231 saboda sun ki umarnin gwamnati na sabunta bayanansu.
Albashin ma'aikata
Samu kari