Gaskiyar Magana Ta Bayyana Kan Rade-Radin Kuma Burmawar Ma’aikata Yajin Aiki a Yau

Gaskiyar Magana Ta Bayyana Kan Rade-Radin Kuma Burmawar Ma’aikata Yajin Aiki a Yau

  • A karshen makon jiya wasu su ka fara yawo da jita-jita a kan maganar komawa yajin-aiki a Najeriya
  • Kungiyoyin ma’aikata na NLC da TUC sun ce labarin ba gaskiya ba ne, kuma mutane su yi watsi da shi
  • Benson Upah ya sanar da al’umma cewa a halin yanzu, ba a tsaida magana a kan tafiya yajin-aiki ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Kungiyar ‘yan kwadagon Najeriya (NLC) da kungiyar ‘yan kasuwa (TUC) sun musanya batun shiga wani sabon yajin-aiki.

An fara rade-radin cewa ma’aikatan Najeriya za su sake komawa yajin-aiki, Tribune ta ce babu kanshin gaskiya a wannan labari.

TUC da NLC
TUC da NLC sun karyata batun yajin-aiki Hoto: NLC
Asali: Facebook

Shugabannin NLC da TUC sun shaida cewa takardar da ake yadawa a kan maganar shiga yajin-aiki sam ba daga hannunsa ya fito ba.

Kara karanta wannan

Muje zuwa: Wata mata ta hango alheri bayan da Dangote ya samu kishiya wajen gina matatar mai

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Babu ruwan 'Yan NLC da TUC

A safiyar Lahadi, Legit ta ci karo da takarda mai dauke da sa hannun Kwamred Emmanuel Ugboaja da kuma Kwamred Nuhu Toro.

Kungiyoyin na NLC da TUC sun ce takardar sanarwa ba gaskiya ba ne, labarin karya ne.

Shugaban sashen yada labarai da hulda da jama’a na NLC da TUC a Najeriya, Mista Benson Upah ya tabbatar da haka a ranar Lahadi.

Benson Upah ya ce jama’a su daina biyewa wannan sanarwa ta karya, su daina ba ta wata kima domin ba su da niyyar tafiya yajin-aiki.

Premium Times ta ce a halin yanzu da ake magana, ‘yan kwadago da ‘yan kasuwan ba su yanke shawarar su dakatar da zuwa aiki ba.

Hakan yana zuwa ne makonni bayan an dawo yajin-aiki a dalilin kara kudin fetur.

Kara karanta wannan

Annobar 'Korona' ta sake dawo wa Najeriya? Gaskiya ta bayyana kan lamarin

Jawabin jami'in kwadago

Muna so mu fito karara mu sanar da cewa NLC ko TUC ba ta amince ko ta bada wani umarnin shiga yajin aiki daga ranar Litinin, 18 ga Disamba ba,
Wannan sanarwa da ake ta yadawa karya ce kacoma kuma jama’a su yi watsi da ita.”

- Benson Upah

Yajin aikin NLC da TUC

A baya an samu rahoto da ya ce kungiyar kwadago ta NLC ta fitar da wasu sharuda da gwamnatin Najeriya za ta cika kafin a sasanta.

NLC ta tafi yajin aiki saboda abin da ya faru da shugabanta, Joe Ajaero a Imo. A dalilin wannan ne ma'aikata suka daina zuwa ofis.

Asali: Legit.ng

Online view pixel