Kudu maso gabashin Najeriya
Yan bindigar da suka sace mamban Majalisar dokokin jihar Anambra. Justice Azuka sun ƙashe shi, an gano gawarsa da ta fara rubewa a gadar Neja ta biyu.
Aregbesola ya yafe wa Olaboye da ya nemi gafara kan yunƙurin kashe shi a 2006. Yayin da ya yiwa mutumin nasiha, tsohon gwamnan ya ce bai rike shi a zuciya ba..
MURIC ta bukaci jami’an tsaro su dauki mataki kan barazanar da ake yi wa Musulmin Kudu maso Yamma da shugabanninsu kan batun kafa shari’ar Musulunci a yankin.
Zaman kotun jihar Imo.ya gamu da tangarda ranar Juma'a, lauyoyi da ma'aikata sun yi rige rigen ficewa daga harabar kotun da suka gano gini ya fara girgiɗi
Oba OmoTooyosi ya ce bai dace a kafa shari'ar Musulunci a Kudu maso Yamma ba, yana mai cewa dimokuradiyya ce kadai za ta tabbatar da zaman lafiya.
Ana ci gaba da ce-ce-ku-ce kan kafa shari'ar Musulunci a Kudu maso Yammacin Najeriya. Yayin da Musulmai suka nuna goyon baya, Yarbawa sun ce ba su yarda ba.
Peter Obi ya ce shi bai kwallafa rai a kan lallai sai ya zama shugaban kasa ba amma yana bukatar Najeriya ta gyaru ta hanyar samar da shugabanci mai inganci.
Rikici ya kara tsananta a PDP yayin da 'yan kwamitin ayyuka na jam'iyyar suka ki amincewa da nadin lauyan da zai kare jam'iyyar a kotun koli, wanda Damagum ya zaba.
Omowunmi Dada ta sha dakyar yayin da ta kamu da cutar sepsis yayin daukar fim a Oyo. An gano cewa cutar tana da matukar hatsari ga rayuwar mutum.
Kudu maso gabashin Najeriya
Samu kari