Shugaba Tinubu Ya Dawo Gida Najeriya Mako Daya Bayan Taron UNGA

Shugaba Tinubu Ya Dawo Gida Najeriya Mako Daya Bayan Taron UNGA

  • Bola Ahmed Tinubu ya dawo Najeriya ranar Jumu'a da daddare mako ɗaya bayan kammala taron UGGA a ƙasar Amurka
  • Ba bu wanda ya san inda shugaban ƙasar ya wuce bayan taron kuma rahoto ya nuna ya baro New York tun 22 ga watan Satumba, 2023
  • Lamarin dai ya haifar da cece-kuce a faɗin Najeriya musamman bayan tawagar da suka raka shi sun dawo Najeriya

FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya dawo gida Najeriya bayan mako ɗaya ba a ji ɗuriyarsa ba, lamarin da ya haifar da cece-kuce a faɗin ƙasar nan.

Tinubu bai dawo gida ba kuma kakakinsa da fadar shugaban ƙasar Najeriya ba su ce komai ba dangane da inda ya wuce bayan kammala taron majalisar ɗinkin duniya a birnin New York.

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
Shugaba Tinubu Ya Dawo Gida Najeriya Mako Daya Bayan Taron UNGA Hoto: Dokin Karfe
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa an shiga damuwa game da inda shugaban ya shiga bayan ganin tawagar da suka raka shi zuwa ƙasar Amurka sun dawo Najeriya ba tare da shi ba.

Kara karanta wannan

Yajin Aiki: Ƙungiyoyin Kwadago Sun Yi Fatali da Taron Da Gwamnatin Tinubu Ta Shirya A Villa

Ministan harkokin ƙasashen waje, Ambasada Yusuf Tuggar, Ministan sadarwa, kirkire-kirkire da tattalin razikin zamani, Bosun Tijjani, na cikin tawagar da suka raka Tinubu Amurka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila, yana cikin waɗanda suka je je taron UNGA tare da Tinubu, amma sun dawo shiru ba a ga shugaban ba.

Ina shugaba Tinubu ya wuce bayan baro ƙasar Amurka?

Kakakin Shugaban Kasa, Ajuri Ngelale, ya yi shiru kan inda Tinubu ya maƙale bayan ya bar New York a ranar 22 ga Satumba, 2023.

Ba a san inda shugaba Tinubu ya wuce ba tun bayan baro ƙasar Amurka har sai da ya dawo Najeriya jiya Jumu'a, 28 ga watan Satumba, 2023 da daddare, NTA News ta tabbatar.

Sai dai wasu rahotanni da ba a tabbatar da ingancinsu ba sun yi iƙirarin cewa Tinubu ya wuce birnin Farisa na ƙasar Faransa bayan ya taso daga New York.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu Ta Kira Zaman Gaggawa da NLC da TUC a Abuja, Bayanai Sun Fito

Gwamnatin Tarayya Ta Gayyaci NLC Da TUC Zuwa Taron Gaggawa a Abuja

A wani rahoton na daban Gwamnatin tarayya ta shirya taron gaggawa da jagororin kungiyoyin kwadago a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Wannan dai wani yunkuri ne na daƙile shirin NLC da TUC na tsunduma yajin aikin sai baba ta gani daga ranar 3 ga watan Oktoba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel