Siyasar Najeriya
Jam'iyyar PDP ta sake yin magana kan halin da yan Najeriya suke ciki dangane da tsadar rayuwa da kuma yadda shugabannin APC suka wawure N20trn a kasar nan.
Gwamna Mai Mala Buni ya ayyana ranar Laraba, 7 ga watan Fabrairu a matsayin da babu aiki domin karrama marigayi tsohon gwamnan jihar da ya rasu a kasar Saudiyya.
Jam'iyyar APC reshen jihar Rivers ta zargi Gwamna Siminalayi Fubara da salwantar da dukiyar al'ummar jihar. Jam'iyyar ta yi zargin cewa ya batar da N144bn.
Taƙaddamar jan ragamar APC reshen jihar Benuwai ta ƙara tsanani yayin da mutum ke ikirarin zama shugaban jam'iyya na jiha, an yi kaca-kaca da babbar sakatariya.
Babban jigon jam'iyya mai kayan daɗi, Farfesa Geoff Onyejegbu, ya ce idan Kwankwaso ya zama shugaban ƙasa, ƴan Najeriya sun gama kuka kan matsalar tsaro.
Wasu yan daba sun yi kokarin hana taron godiya domin nuna farin ciki bisa nasarar da Allah ya ba Gwamna Fubara a hukuncin kotun koli amma ba su ci nasara ba.
Sanata Oluremi Tinubu, mai ɗakin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ta gana da matan gwamnonin Najeriya a fadar shugaban ƙasa da ke birnin tarayya Abuja.
Babbar kotun tarayya mai zama a Abuja ta yi watsi da zancen bada belin mutum biyar masu biyayya ga Gwamna Fubara, waɗanda ake zargi da hannu a ayyukan ta'addanci
Alex Kadiri yana ganin babu dalilin da Yahaya Bello zai rike APC. Tsohon sanatan na Kogi bai goyon bayan tsohon gwamnansa ya maye gurbin Abdullahi Ganduje.
Siyasar Najeriya
Samu kari