Siyasar Najeriya
Majalisar dattawa ta fara shirin tantance mutum 7 da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya naɗa a matsayin sababbin ministoci bayan ya yi garambawul.
Fadar shugaban ƙasa ta musanta raɗe-raɗen cewa shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi kane-kane da kujerar ministan man fetur, Onanuga ya faɗi gaskiya.
A ranar Laraba Bola Tinubu ya tabbatar da korar ministoci 5 daga aiki tare da naɗa wasu sababbi, ya masu fatan alheri a duk lamurran da suka tasa a gaba.
Sahugaban PDP ya ce wahalhalun da 'yan Najeriya ke ciki na da nasaba da rashin kwarewa da halin ko in kula na shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na Najeriya.
Wani babban kusa a jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ya bukaci 'yan Arewa da su marawa Shugaba Bola Tinubu da Kashim Shettima baya a zaben 2027.
Shugaban cocin INRI, Primate Elijah Ayodele ya soki garambawul da Shugaba Tinubu ya yi a majalisar ministocin kasar nan, inda ya ce ba wadanda ya kamata aka kora ba.
Dan gwagwarmaya a yankin Kudu maso Kudu, Alhaji Asari Dokubo ya bayyana irin nadamar da ya yi wurin goyon bayan Bola Tinubu a zaben 2023 a Najeriya.
Rahotanni sun tabbatar da cewa wasu manyan shugabannin siyasa a Arewacin Najeriya sun fara ganawa domin neman wanda za su goyawa baya a zaben 2027.
A karshe dai jam'iyyar NNPP ta yi nasarar lallasa dukkan jam'iyyun adawa a Kano, ta lashe kujerun ciyamomo da kansiloli gaba ɗaya a zsben da aka yi yau Asabar.
Siyasar Najeriya
Samu kari