El Rufai, Ministan Tinubu da Wasu Ƴan Siyasa da Suka Mallaki Gidajen Tiriliyan 1.49 a Dubai

El Rufai, Ministan Tinubu da Wasu Ƴan Siyasa da Suka Mallaki Gidajen Tiriliyan 1.49 a Dubai

Wani rahoto ya nuna cewa kimanin ƴan siyasa 200 a Najeriya da wasu jami'an tsaro ne suka mallaki manyan gidaje/kadarori da suka kai na $1bn (N1.49trn) a Dubai.

Ana zargin ƴan siyasa da manyan jiga-jigai ƴan asalin Najeriya sun sayi waɗannan kadarori na alfarma a birnin Dubai a cikin shekaru ƙasa da 20.

El-Rufai, Fagbemi da Atiku.
Bincike ya bankado wasu manyan kadarori na ƴan Najeriya a Dubai Hoto: Nasir El-Rufai, Lateef Fagbemi, Atiku Abubakar
Asali: Facebook

An bankado kadarorin ƴan Najeriya a Dubai

Rahoton ya nuna cewa mata da ƴaƴan fitattun ƴan siyasar Najeriya, alkalan kotu da wasu manyan jami'an gwamnati na cikin waɗanda suka mallaki kadarori 1,600 a Dubai.

Dubai shi ne birni mafi girma da yawan al'umma a Haɗaɗdiyar Daular Larabawa (UAE).

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda Bussiness Day ta ruwaito, an gano hakan ne a wani bincike da aka shafe watanni shida ana yi ƙarƙashin jagorancin kungiyar yaƙi da rashawa OCCRP.

Kara karanta wannan

Fulani makiyaya sun yi magana kan batun tsige Sarkin Musulmi, sun yi gargadi

"Galibin kadarorin suna wurare kamar Burj Khalifa, gini mafi tsayi a duniya; Marsa Dubai, Al Merkadh, Palm Jumeirah, Wadi Al Safa, Madinat Al Mataar, Nad Al Shiba First da sauransu."
"Bincike ya nuna cewa ƴan Najeriya maza sun yi rijista da sunan mata yayin da matan suka yi rijistar kadarorin da sunan maza," in ji rahoton.

Daily Trust ta ce rahoton ba wai tuhuma ba ce ga ƴan siyasar da sunayensu suka fito saboda babu wani kwakƙwaran dalili da ke nuna da kuɗin sata suka saya.

Legit Hausa ta tattaro muku wasu daga ciki, ga su kamar haka:

1. Atiku Abubakar

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya mallaki gida mai ɗaki uku wanda aka kiyasta kudinsa ya kai $1.23m a Palm Tower da ke Dubai.

2. Ɗiyar Atiku ƴar shekara 23

Rahoton ya ce ɗiyar Atiku Abubakar mai shekaru 23 ta mallaki wani gida mai daki daya a Trade Center Second, wanda kudinsa ya kai $104,135.

Kara karanta wannan

An ba alkalai cin hanci a shari'ar zaben shugaban kasa na 2023? Gaskiya ta bayyana

Har ila yau ta mallaki wani gidan na daban mai daki biyu a Hadaeq Sheikh Mohammed Bin Rashid wanda aka kiyasta ya kai $289,305.75.

3. Lateef Fagbemi

Rahoton ya kuma bayyana cewa Antoni-Janar kuma ministan shari'a, Lateef Fagbemi ya mallaki kadarar $85,846 a Al Hebiah Third.

4. Malam Nasir El-Rufa'i

An gano cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai, ya mallaki wani gida mai daki hudu wanda kudinsa ya kai $193,084 a Al Hebiah Third.

5. Yusuf Datti Baba-Ahmed

Jigon Labour Party (LP) kuma mataimakin Peter Obi a zaben shugaban kasa na 2023, Yusuf Datti Baba-Ahmed, yana cikin waɗanda sunayensu suka fito.

An gano kadarori takwas da darajarsu ta kai $2.28m na fitaccen dan siyasar kuma dan kasuwa.

Kadarorin suna wurare kamar Burj Khalifa, Al Yelaiss, Al Barsha South Fourth, da Town Square Safi 2.

6. Attahiru Bafarawa

An alakanta tsohon gwamnan jihar Sakkwato, Attahiru Bafarawa da wasu kadarori bakwai da kudinsu ya kai $1.48m.

Kara karanta wannan

Katsina: An kama mutum 2 da hannu a sace mahaifiyar Dauda Kahutu Rarara

Bugu da kari, matarsa ​​ta mallaki wani tafkeken gida da ke Palm Jumeirah, wanda darajarsa ta kai $750,112.

7. Sanata Ibrahim Folorunsho Jimoh

Bincike ya nuna cewa Sanata Ibrahim Folorunsho Jimoh mai wakiltar Ondo ta Kudu ya mallaki kadarori bakwai a Dubai.

8. Sanata Ike Ekweremadu

Haka nan kuma an gano wasu kadarori biyar na Ike Ekweremadu, tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, wanda yanzu haka yake zaman gidan yari a kasar Ingila.

9. Mohammed Sidi Sani

An gano wani gida da ke Marsa Dubai, wanda ƙimarsa ta kai $590,807 na da alaƙa da tsohon darakta-janar na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) wanda aka kora a watan Afrilun 2023.

10. Ashe Ahmadu Mu'azu

Matar tsohon shugaban jam'iyyar PDP, ta mallaki wata kadara da ke Hadaeq Sheikh Mohammed Bin Rashid, wanda ta kai dala Dala miliyan 1.16.

11. Ahmed Maƙarfi

An gano wata kadara a Burj Khalifa da ta kai $822,016 mallakin tsohon gwamnan Kaduna, Ahmed Makarfi.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka jami'an tsaro, sun sace mutum 20 a Kaduna

Za a fara shari'ar Kwankwaso da EFCC

A wani rahoton kuma Rabiu Kwankwaso da wasu mutum bakwai sun shigar da ƙarar hukumar EFCC gaban babbar kotun jihar Kano kan yunƙurin take haƙƙinsu.

Yayin da aka gabatar masa da ƙarar, mai shari'a Yusuf Ubale ya sanar da cewa kotu za ta fara sauraron ƙarar ranar 11 ga watan Yuli, 2024.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262