"Neman Kifar da Tinubu Ne": Shettima Ya Zargi Musabbabin Ziyarar Kwankwaso ga El Rufai
- Kungiyar matasan Arewa ta AYCF ta zargi ziyarar Rabiu Kwankwaso ga Nasir El-Rufai a matsayin kulle-kullen siyasa saboda zaben 2027
- Shugaban kungiyar, Yerima Shettima shi ya yi wannan zargi inda ya ce kowa yana da damar ziyartar duk wanda yake so
- Shettima ya bayyana haka ne yayin da ya ke martani kan ziyarce-ziyarce da ake yawan samu na ƴan siyasa a yanzu
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Kungiyar Arewa Youth Consultative Forum (AYCF) ta yi martani kan ziyarar Rabiu Kwankwaso ga Nasir El-Rufai.
Kungiyar ta ce hakan bai rasa nasaba da neman tuge shugaban kasa Bola Tinubu a zaben 2027 da ake tunkara.
Ƙungiya ta soki ziyarar Kwankwaso ga El-Rufai
Shugaban kungiyar, Yerima Shettima shiga ya bayyana haka a karshen mako yayin hira da jaridar Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shettima ya ce El-Rufai yana da ƴancin ziyartar duk wanda ya ke so, amma wannan ziyara akwai kulle-kullen siyasa a ciki.
"Akwai kulle-kullen siyasa", Kungiya kan ziyarce-ziyarce
"Babu wata matsala a ziyarar da El-Rufai ya ke yi saboda yana da ƴancin yin haka ga wanda ya so."
"Amma wannan ziyarar da ƴan adawa ke yi akwai kulle-kullen siyasa a ciki musamman saboda zaben 2027."
"Idan ba a mantaba, El-Rufai ya kai ziyara ga jam'iyyar SDP sannan ya kai wa Buhari ziyara a gidansa da ke Daura."
"Sannan haduwarsa da Rabiu Kwankwaso akwai siyasa a ciki da kuma neman yadda za su kwace mulki a hannun Bola Tinubu."
- Yerima Shettima
Kwankwaso ya ziyarci El-Rufai a gidansa
A wani labarin, kun ji cewa Sanata Rabiu Kwankwaso ya kai ziyara ta musamman ga tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai.
Ƴan Najeriya da dama sun yi tofa albarkacin bakinsu inda suke zargin ziyarar ba ta rasa nasaba da zaben 2027 mai zuwa.
Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan ziyarar da El-Rufai ya kai wa tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari a gidansa da ke Daura.
Asali: Legit.ng