Najeriya Za Ta Samu Bashin $150Bn da Halatta Auren Jinsi a Yarjejeniyar Samoa?

Najeriya Za Ta Samu Bashin $150Bn da Halatta Auren Jinsi a Yarjejeniyar Samoa?

  • Gwamnatin tarayya ta sake fitowa ta kare kanta daga zargin ta amince da auren jinsi da kuma karbar bashin $150m a yarjejeniyar Samoa
  • Ministan yada labarai da takwaransa na kasafin kudi ne suka kare gwamnatin a wani taron gaggawa da suka gudanar a birnin Abuja
  • Gwamnatin ta ce wasu jaridu ne kawai ke zuzuta batun yarjejeniyar Samoa saboda su sanya tsanar Tinubu a zukatan 'yan Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Gwamnatin tarayya ta ce babu wani lamunin $150bn ko kuma amincewa da 'yancin ‘yan madigo, 'yan luwadi, 'yan daudu, da masu auren jinsi a cikin yarjejeniyar Samoa.

Gwamnatin ta ce yarjejeniyar Samoa hadin gwiwa ce tsakanin tarayyar Turai da kasashen Afirka, Caribbean da Pasifik, wadda za ta bunkasa zamantakewa da tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Samoa: Tinubu zai dauki mataki kan Daily Trust game da rahoton yarjejeniyar da aka yi

Gwamnati ta yi magana kan yarjejeniyar Samoa
Gwamnati ta ce babu auren jinsi ko lamunin $150bn a cikin yarjejeniyar Samo. Hoto: @HMMohammedIdris
Asali: Twitter

Akwai saɗarar auren jinsi a Samoa?

Ministan yada labarai, Mohammed Idris da takwaransa na kasafin kudi, Sanata Atiku Bagudu ne suka bayyana hakan a wani taron da suka yi a Abuja, inji rahoton Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Babu wata saɗara da ke a cikin yarjejeniyar Samoa da ta nemi Najeriya ta amince da 'yancin auren jinsi (LGBTQ)," inji Alhaji Mohammed.

Ministan yada labaran ya kara cewa:

"Shugaba Bola Tinubu ya na sane da kimar 'yan Najeriya kuma ba zai yi wani abu da zai yi wasa da hankalinsu ba."

Samoa: "Babu bashin $150bn" - Bagudu

Har ila yau, a kan zargin Najeriya za ta samu $150bn daga yarjejeniyar Samoa, ministan kasafi, Sanata Bagudu ya ce babu irin wannan tanadi a cikin yarjejeniyar.

Sanata Bagudu ya ce Najeriya ta kafa sharadin cewa duk wani tanadi na yarjejeniyar da ya sabawa tanade-tanaden kundin tsarin mulkin Najeriya ba zai samu karbuwa ba.

Kara karanta wannan

Lauya ta fayyace matsayar yarjejeniyar Samoa wajen kawo auren jinsi a Najeriya

Jaridar Tribune ta ruwaito ministan ya ce Najeriya ta sanya hannu kan yarjejeniyar ne saboda fa'idodinta ga kasar da suka hada da, ilimi, 'yancin ɗan adam, da kuma tattalin arziki

Gwamnati ta soki jaridu kan Samoa

Gwamnatin tarayya ta kuma zargi wasu kafafen yada labarai da wallafa bayanan karya da tunzura jama'a kan yarjejeniyar Samoa.

Ministan yada labarai ya yi ikirarin cewa ana zuzuta maganar ne kawai domin a sanya tsanar gwamnatin Shugaba Tinubu a zukatan 'yan Najeriya.

Sheikh Gumi ya yi martani kan Samoa

A wani labarin, mun ruwaito cewa, fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Ahmed Gumi ya yi magana kan cece-kucen da ake yi game da yarjejeniyar Samoa.

Malamin ya ce ya duba yarjejeniyar kuma tabbas babu auren jinsi a ciki amma yana fargabar sau gwamnatin Najeriya ta je karbar kudi ne za a tilastata halatta dokar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.