"Tuna Halacci Ke Hana Ni Ɗaukar Wasu Matakai": Gwamna ga Mai Gidansa

"Tuna Halacci Ke Hana Ni Ɗaukar Wasu Matakai": Gwamna ga Mai Gidansa

  • Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara ya yi martani kan zarginsa da ake yi kan butulci ga wadanda suka taimake shi
  • Gwamnan ya ce babu inda ya yi butulci kuma sanin halacci ne ma ke hana shi daukar wasu tsauraran matakai
  • Fubara ya bayyana haka ne a jiya Litinin 8 ga watan Yulin 2024 yayin taron sakarakuna da shugabannin kabilar Ikwerre

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Rivers - Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers ya yi martani kan dambarwa tsakaninsa da Nyesom Wike.

Gwamnan ya ce tuna halaccin da aka masa ne yake hana shi daukar wasu matakai masu tsauri.

Gwamna ya fayyace gaskiya da zarginsa da butulci
Gwamna Siminalayi Fubara ya ce tuna halacci ke hana shi daukar wasu matakai. Hoto: Nyesom Wike, Siminalayi Fubara.
Asali: Facebook

Fubara ya wanke kansa daga zargin butulci

Kara karanta wannan

"Ban san meye LGBTQ ba": Jami'in Hisbah ya magantu bayan kama shi da tallata auren jinsi

Fubara ya bayyana haka ne yayin wani taro da ƴan kabilar Ikwerre da sarakunansu a jiya Litinin 8 ga watan Yulin 2024, cewar Channels TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan ya ce duk da abubuwan da suke faruwa na siyasa ba zai gajiya ba wurin ayyukan alheri a jihar ba dare ba rana.

Har ila yau, ya ce zai ci gaba da mutunta kowa kamar yadda ya ke ba tare da bambanci ba, Vanguard ta tattaro.

Gwamna Fubara koka kan yadda ake zarginsa

"Bari in sake fadan wanna magana, Fubara ba butulu ba ne, idan da ni mutumin banza ne ba zan iya boyewa na tsawon lokaci ba."
"Ba zan iya boyewa na mako daya ko shekara biyu ko takwas ba, a shekaru 16 idan da ni mutumin banza ne da an gane."
"Mene wannan mugun hali da butulci da Fubara ya nuna? amma na bar komai ga Ubangiji wanda shi ne zai yi hukunci."

Kara karanta wannan

"Yafi yiwa yankinsa illa kamar Buhari": An fadi yadda tsare-tsaren Tinubu ke kassara Najeriya

- Siminalayi Fubara

Fubara ta kalubalanci Wike

Kun ji cewa Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers ya kalubalanci Ministan Abuja, Ministan Abuja, Nyesom Wike a jihar.

Fubara ya ce ayyukan da ya yi cikin shekara daya yafi shekaru takwas na gwamnatoci da dama da suka shude a jihar.

Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da takun saka tsakanin Gwamna Fubara da mai gidansa, Nyesom Wike wanda a yanzu Ministan Abuja ne..

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.