Siyasar Najeriya
A labarin nan, za a ji Mawaki Dauda Kahutu Rarara ya ce dole mutum ya rika tuna tushensa tare da yin aikin alheri domin gode wa ni'imar da Allah SWT ya yi masa.
Kwamitin tantancewa na APC ya cire Omisore da wasu mutum shida daga takarar fitar da gwani na zaben kujerar gwamnan jihar Osun saboda matsalolin takardu.
Mambobi 16 na majalisar dokokin jihar Rivers sun fice daga jam'iyyar PDP zuwa APC, inda kakakin majalisa Martin Amaewhule ya jagoranci sauya shekar.
A labarin nan, za a ji yadda Atiku Abubakar ya bayyana damuwa kan naɗin Farfesa Mahmoud Yakubu da yadda zai kawo cikas ga dimokuraɗiyy a Najeriya.
A labarin nan, za a ji cewa gwamnatin tarayya ta barranta kanta daga dukkanin wani yunkuri na fara kamfen gabanin zaben 2027, ta ce motocin da ake gani na masoya ne.
Kungiyar kwadago ta NLC ta ce za ta gudanar da zaman makoki da zanga-zanga a Najeriya. 'Yan kwadago sun ce ba za su zuba ido ana cigaba da kashe mutane ba.
Jam'iyyar APC mai adawa a jihar Zamfara ta gamu da koma baya bayan wasu daga cikin 'yan majalisar da take da su sun yi murabus. Sun bayyana dalilansu.
An tsige shugaban jam'iyyar APC na jihar Cross River, Alphonsus Ogar Eba bayan kuri’ar rashin amincewa da mulkinsa bia zargin almundahana da rufe ofis.
Gwamnan jihar Rivers, Sir Siminalayi Fubara ya kara samun sabani da 'yan majalisar jihar da ke yi wa Wike biyayya. Fubara ya musu martani kan daukar ma'aikata.
Siyasar Najeriya
Samu kari