Siyasar Arewa
A labarin nan, za a ji cewa tsohon mataimakin gwamnan Jigawa, Alhaji Ahmed Mahmud Gumel ya zama jagoran ADC, kuma ya nemi matasa su shigo jam'iyyar.
Tsohon shugaban PDP na jihar Katsina, Hon. Salisu Lawal Uli, ya ce ya gaji da zama a jam'iyyar da shugabancinta ke tangal tangal, ya sanar da komawa haɗakar ADC.
Kungiyar matasan Arewa ta ce har yanzun shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu na da cikakken goyon bayan ƴan Arewa, ta yi watsi da ikirarim ɗiyar Buba Galadima.
Shafin yanar gizon ADC ya gamu da yawan masu shiga domin yin rajista, lamarin da ya jawo ya lalace sau uku a cikin mako daya. ADC na son zama babbar jam'iyyar adawa.
Adamu Waziri, tsohon ministan Najeriya, ya fice daga jam'iyyar PDP zuwa ADC don neman shugabanci na nagar saboda damuwar rashin tsaro da halin tattalin arziki.
Zainab Buba Galadima ta Bola Tinubu zai fuskanci babban kalubale a Arewa a zaben 2027. Ta ce mutane da yawa ba za su zabe shi ba, zai samu kuri'a kashi 30 kawai.
Sanata Lamiɗo na shirin barin APC zuwa ADC kafin 2027, yayin da jita-jita ke karfi kan rashin jituwa da jagororin APC a jihar Sakkwato a Arewacin kasar nan.
Wani hadimin gwamnan jihar Yobe a Arewacin Najeriya ya yi murabus daga mukaminsa inda ya sauya sheka zuwa jam'iyyar ADC da aka ƙaddamar saboda hadaka.
Gwamnan Borno, Babagana Zulum ya karyata jita-jitar sauya sheka zuwa ADC da wasu gwamnoni biyar, ya ce ƙarya ce kuma yana mai biyayya ga APC don ci gaban Borno.
Siyasar Arewa
Samu kari