Labaran NNPC
Ministan harkar wuta ya fito ya yi dogon bayani a game da durkushewar babban layin lantarki, Adebayo Adelabu ya ce matsala ce aka samu, hakan ya yi sanadiyyar cikas.
Olusegun Obasanjo ya na ganin maganar matatar man Fatawal ta fara aiki a shekarar nan kanzon kurege ne, ya ce Bola Tinubu ya daina yaudarar kan shi kan matatun.
Shugaban kamfanin mai na NNPC. Mele Kyari ya bayyana yadda kamfanin ya yi asara bayan raguwar amfani da mai a kasar da kaso 30 cikin dari bayan cire tallafi.
Babban malamin addinin kiristanci, Primate Elijah Ayodele, ya bayyana cewa Najeriya ba za ta iya matsawa gaba ba har sai Shugaba Tinubu ya gudanar da bincike.
Ana kyautata zaton shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu zai iya bin tafarkin Buhari wajen rike kujerar Ministan man fetur a Najeriya a wannan mulkin nasa da ake.
A wani rahoto da aka fitar, Najeriya ta yi asarar fiye da Dala biliyan 46 saboda satar danyen mai da ake yi a kasar, a cikin mako daya, an samu satar sau 114.
Kamfanin NNPC ya karbi bashin Dala biliyan uku a bankin AFRIEXIM da ke kasar Masar don kawo daidaito a farashin Naira da kuma kasuwannin canjin kudade a kasar.
Gwamnatin tarayya ta karkashin BPE, za tayi gwanjon kayan gwamnati da nufin samun kudi. Dama Atiku Abubakar ya na da ra’ayin a cefanar da irinsu kamfanin NNPC.
Kamfanin man fetur na Najeriya wato NNPC ya yi watsi da rahotannin kafofin watsa labarai na baya bayan nan cewa za a kara farashin man fetur zuwa N720 ko N750.
Labaran NNPC
Samu kari