Ana Bin Kowane Dan Najeriya Bashin N410,000 In Ji Rahoton Hukumar Kididdiga

Ana Bin Kowane Dan Najeriya Bashin N410,000 In Ji Rahoton Hukumar Kididdiga

  • Hukumar ƙididdiga ta ƙasa (NBS), ta bayyana yawan bashin da ake bin Najeriya daga shekarar 2015 zuwa yau
  • Hukumar ta bayyana cewa kowane ɗan Najeriya zai biya naira 410,000 kafin ƙasar ta iya fita daga kangin da take ciki
  • Sai dai hukumar ta nuna cewa yawan masu fama da rashin aikin yi ya ragu a kan yadda yake a shekarun baya

An bayyana cewa a yanzu haka bashin da ake bin Najeriya ya kai dala biliyan 113.42, wanda ya yi daidai da naira tiriliyan 87.38 a kuɗin ƙasar.

Hukumar ƙididdiga ta ƙasa (NBS) ce ta bayyana hakan, a cikin wani rahoto da aka wallafa ranar Juma'a, a shafin Statisense na X da aka fi sani da Twitter a baya.

An bayyana yawan bashin da ake bin Najeriya
Kowane dan Najeriya zai biya naira 410,000 kafin a biya bashin da ake bin ƙasar. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Yawan kuɗaɗen da ake bin kowane ɗan Najeriya

Kara karanta wannan

Shin Da Gaske CBN Na Son Sauya Fasalin Naira Domin Ta Dawo Daidai Da Dala? Bayanai Sun Fito

Rahoton ya bayyana cewa bashin da ake bin Najeriya ya karu da kashi 622% a cikin shekaru takwas din da suka gabata, wato daga 2015 zuwa 2023 kenan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Haka nan kuma hauhawar farashin kayayyaki ya ƙaru da kashi 25%, yayin da rashin aikin yi a cewar rahoton, ya dawo kashi 4.1% a cikin shekarar 2023 da muke ciki.

A shekarar 2015, naira 66,000 ne ake bin kowane mutum ɗaya a Najeriya, amma a yanzu duk mutum ɗaya sai ya ba da naira 410,000 kafin a iya biyawa Najeriya bashi.

Miji da mata za su biya naira 820,000, idan kuma suna da ɗa guda ɗaya za su biya naira miliyan 1.23, idan yara biyu ne za su biya naira miliyan 1.64.

NNPCL ya bayyana ribar da ya samu a farkon shekarar 2023

Kara karanta wannan

"Ban Taɓa Ganin Naira Biliyan 1 a Asusun Banki Na Ba Har Na Bar Mulki" Tsohon Gwamnan Arewa

A baya Legit Hausa ta yi rahoto kan maƙudan kuɗaɗen da kamfanin mai na Najeriya, NNPCL ya ce ya samu a farkon shekarar nan ta 2023 da muke ciki.

Manajan daraktan kamfanin, Mele Kyari da yake jawabi a gaban kwamitin majalisa, ya bayyana cewa kamfanin ya samu ribar naira biliyan 18.4 a wannan shekarar.

Ya ce wannan gagarumar nasara ta samo asali ne daga fadada gami da inganta harkoki da kamfanin na NNPCL ya yi.

An bayyana irin halin da shugaba Tinubu ya karɓi Najeriya a ciki

Legit Hausa ta yi rahoto a baya kan yadda Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya karɓi tattalin arziƙin Najeriya a ciki.

An bayyana cewa shugaban ya samu ƙasar ne a cikin mummunan yanayi na tattalin arziƙi, da kuma rashin aikin yi da ya yi ma ta katutu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel