Labaran NNPC
Bayan kara tsadar litar man fetur, layin ababen haea ya cika gidajen mai maƙil musamman waɗanda ba su kara farashi ba har kawo yanzu a Kano da birnin Abuja.
An ga motoci na kama gabansu daga gidan man kamfanin mai na ƙasa NNPCL da ke Hotoro a cikin garin Kano bayan samun labarin farashin litar mai ta ƙara tsada.
Bincike ya nuna cew an ƙara tashin farashin litar man fetur daga N539 zuwa samanda N600 a birnin tarayya Abuja, an gano cewa farashin ya kai naira 617 yau.
Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa nan ba da jimawa ba farashin mai zai karye yayin da dillalan man fetur suka fara shigo da man cikin Najeriya don wadatuwar shi
A. A Rano ya musanya labarin da ake yadawa cewa ya karya farashin fetur. Dama zai yi wahala a iya saida litar fetur a N400 domin bincikenmu ya nuna akasin haka.
Fetur zai iya tashi a Najeriya a lokacin da mutane ba su gama farfadowa daga radadin cire tallafi ba. A wurare da-dama lita ta kai N540, kudin ya fara wuce haka
Ana kyautata zaton Bola Ahmed Tinubu ya nada kwamiti da zai binciki gaskiyar ayyukan NNPCL. Shugaba Tinubu ya kafa kwamitin binciken sabanin NNPCL da FAAC.
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ƙulla yarjejeniya da wasu ƙasashen nahiyar Afirika domin kawo ƙarshen mamaye kasuwar iskar gas ta Rasha a nahiyar Turai.
Rahotanni sun tabbatar da cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, bai dakatar da Malam Mele Kyari ba daga shugabancin kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL).
Labaran NNPC
Samu kari