Fadar shugaban kasa
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya sauke wasu shugabannin hukumomin gwamnatin tarayya biyu, waɗanda tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ya nada.
Fadar shugaban kasa ta soke katin dakatacciyar ministar jin kai, Dr Betta Edu wanda shi ke ba ta damar shiga Villa. Wannan matakin zai hana ta ganin Tinubu.
Ana tsaka da tsadar man fetur a Najeriya, Shugaba Tinubu ya tura wa shugaban NNPC sako a ranar Litinin. Tinubu ya taya Mele Kyari murnar cika shekaru 59.
Ganin an cire tallafin man fetur Shugaban kasa ya ba ‘Yan majalisa N57.8bn a ba talakawa shinkafa. Ana zargin wasu 'yan majalisa sun boye shinkafar da aka ba su.
Za a kashe makudan kudi da sunan gyare-gyare a majalisar tarayya. Face-face, gyare-gyare da ‘yan kwaskwarima a nan da can za su ci Biliyoyin kudi a majalisar.
Shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa hangensa na cimma tattalin arziki mai girma a Najeriya zai shiga haɗari idan tsaro bai samu ba.
Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya sha ruwan yabo daga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu. Shugaban ya taya gwamnan murnar cika shekara 61 da haihuwa.
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa ba shi da burin da ya wuce ya gina al'umma mai cike da gaskiya da adalci da kawar da rashin haɗin kai.
Bola Ahmed Tinubu ya sanya hannu a kasafin kudin sabuwar shekara 2024 wanda aka yi ƙiyasin zai laƙume N28.78tr a fadar shugaban kasa da ke birnin Abuja.
Fadar shugaban kasa
Samu kari