Shugaba Tinubu Ya Rattaɓa Hannu Kan Kasafin Kudin 2024 a Aso Villa, Bayanai Sun Fito

Shugaba Tinubu Ya Rattaɓa Hannu Kan Kasafin Kudin 2024 a Aso Villa, Bayanai Sun Fito

  • Bola Ahmed Tinubu ya sanya hannu kan kasafin kuɗin shekarar 2024 ya zama doka daga yau Litinin, 1 ga watan Janairu
  • Shugaban ƙasan ya dira ofishinsa da misalin karfe 2:00 na rana kuma kai tsaye ya wuce ɗakin bikin sa hannu kan kasafin
  • Manyan kusoshin gwamnati da suka haɗa da Sanata Akpabio da Tajudeen Abbas sun halarci bikin a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ranar Litinin da yamma ya sanya hannu kan kasafin kudin shekarar 2024 na Naira tiriliyan 28.78 a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Shugaba Tinubu, wanda ya isa ofishinsa bayan sauka a filin jirgin sama da misalin karfe biyu na rana, kai tsaye ya nufi wajen bikin sanya hannu a kan kasafin kudin.

Kara karanta wannan

Mataimakin shugaban majalisar dattawa ya raba motoci 60 a jihar Kano, ya faɗi muhimmin dalili 1

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
Shugaba Tinubu Ya Rattaba Hannu Kan Kasafin Kudin 2024 Na N28.78tr Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Ya rattaɓa hannu a kan kudin kasafin shekarar 2024 ya zama doka a gaban manyan jiga-jigai da ƙusoshin gwamnatin tarayya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayo Onanuga, mai bai wa shugaban ƙasa shawara ta musamman kan harkokin yaɗa labarai da dabaru ne ya tabbatar da haka a shafinsa na manhajar X watau Twitter.

Jiga-Jigan da suka shaida sa hannu a kasafin

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, da kakakin majalisar wakilan tarayya, Honorabul Tajudeen Abbas, sun halarci bikin sanya hannu kan kasafin.

Ministan kudi da harkokin tattalin arziƙi, Mista Wale Edun, ministan kasafi da tsare-tsaren tattalin arziki, Alhaji Atiku Bagudu, da mai bada shawara kan tsaron ƙasa, Nuhu Ribaɗu, sun halarci wurin.

Sauran waɗanda aka gani a wurin bikin sa hannu kan kasafin sune shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila, da shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Dakta Abdullahu Ganduje.

Kara karanta wannan

2024: Shugaba Tinubu ya bayyana babban buri ɗaya tal da ya sa ya nemi hawa mulki sau 3 a Najeriya

Bugu da ƙari, shugaban kwamitin kasafin kuɗin ƙasa na majalisar dattawa, Sanata Olamilekan Adeola, da sauran wasu ƙusoshin FG sun shaida sa hannun Tinubu a kan kasafin.

Legit Hausa ta nemi jin ta bakin wasu ƴan Najeriya kan wannan zunzurutun kuɗi da Gwamnatin Bola Tinubu ta tsara kashewa a shekarar 2024.

Wani malamin Firamare, Abubakar Abdul, ya shaida wa Legit Hausa cewa suna yi wa shugaban ƙasa fatan alheri kuma zasu jira su ga yadda kasafin zai amfani ƴan ƙaaa.

A cewarsa, an daɗe aka ruwa ƙasa na shanyewa amma duk da haka ƴan Najeriya ba zasu cire tsammani da samun sauyi mai amfani ba a wannan lokaci na wahala.

Nura Aliyu, ma'aikacin gwamnati kuma mazaunin Kaduna ya ce kasafin kuɗin ya zo da sauyi mai ma'ana a bangarori da dama yayin da ana nan jiya iyau a wasu ɓangaren.

Ya ce:

"Har yanzun zaka ga kasafin Najeriya na kunshe da kashe-kashen kuɗin masu rike da madafun iko, babu sauyi a nan ɓangaren amma duk da haka muna fatan alheri.

Kara karanta wannan

Sabuwar shekara: Manyan alkawurra 5 da Tinubu ya daukar wa 'yan Najeriya a 2024

Ya kamata shugaban INEC ya yi murabus

A wani rahoton na daban Yadda babban zaɓen 2023 ya gudana kaɗai ya isa ya sa shugaban hukumar zabe ta ƙasa (INEC), Farfesa Mahmud Yakubu, yin murabus.

Farfesa Jideofor Adibe na jami'ar jihar Nasarawa ne ya bayyana haka bisa wasu hujjoji da ya dogara da su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel