Malaman Izala da darika
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi ta'aziyyar shugaban majalisar Musulunci a Najeriya, Sheikh Abdur Rasheed Hadiyyatullah Iwo da ya rasu a Kudancin Najeriya.
Shugaba Bola Tinubu ya kadu da rasuwar Sheikh Mainasara Habibi, yana mai yaba wa da gudummuwarsa a addini, ya kuma roƙi Allah ya gafarta masa kura-kuransa.
Rahotanni sun bayyana cewa Allah ya yi wa mahaifiyar fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Musa Asadus Sunnah rasuwa. Za a yi jana'iza a Kinkinau, Kaduna.
A farkon shekarar 2025, an rasa manyan malaman addinin Musulunci. Rasuwarsu ta bar babban gibi saboda rawar da suke takawa wajen ayyukan da'awah.
Kungiyar Izala ta yi sababbin nade nade. Sheikh Sani Yahaya Jingir ya nada Malam Dalhatu Abubakar Hakimi a gurbin marigayi Sheikh Saidu Hassan Jingir.
Babban malamin Izala, Imam Bello Jandutsi ya rasu a Birnin Kebbi bayan shekaru 30 yana limanci da da’awa. Za a yi jana’izarsa a masallacin Sheikh Abbas, Rafin Atiku.
Sheikh Yusuf Sambo Rigachukun ya yi kra ga Sheikh Sani Yahaya Jingir da Sheikh Abdullahi Bala Lau da su sake haduwa waje daya. Dr Jalo Jalingo ya goyi bayan kiran.
Rundunar 'yan sandan jihar Bauchi ta tafi da wani limamin Juma'a, Ahmad Isa Jaja da ya yi batanci wa Dr Idris Dutsen Tanshi a unguwar Jahun kafin matasa su masa duka
Malaman addinin musulunci a kasar nan sun bayyana kaduwa da samun labarin rasuwar daya daga cikinsu, Sheikh AbdulAzeez Dutsen Tanshi, wanda ya rasu a Bauchi.
Malaman Izala da darika
Samu kari