Hukumar Sojin Najeriya
Rahotanni daga Kaduna sun bayyana cewa akalla gawar mutane 10 aka gano bayan wasu da ake zargin yan fashin daji ne sun kai farmaki yankin Zangon Kataf a jihar.
Wasu tsagerun yan bindiga sun kutsa kai rukunin gidajen Grow homes estate da ke yankin Kubuwa a babban birnin tarayya Abuja, sun yi garkuwa da akalla mazauna 9.
Rundunar sojin Najeriya ta bayyana yadda ta shawo kan lamarin tsaro da ya kunno kai a lokacin da 'yan ta'adda suka so kai hari kan masu akda kuri'u a kasar.
Jami'an rundunar sojin Najeriya sun kai samamen kwantan bauta kan mafakar masu garkuwa da mutane a Kuros Riba, sun ceto kwamishinar harkokin mata da aka sace.
Jiragen yaƙin sojojin sama na Najeriya sun halaka wata mata mai ɗauke da juna da wasu ƙananan yara a jihar Kaduna. Sojojin dai sun biyo wasu ƴan bindiga ne.
Rahotanni daga yankin ƙaramar hukumar Birnin Gwari a jihar Kaduna sun nuna cewa wasu miyagu sun kashe Yan bijilanti 6 a shingen binciken ababen hawan Awaro.
Wasu mahara da ake kyautata zaton sun je ɗaukar fansa ne sun halaka Malamin Coci, Musa Hyok, da 'ya'yansa biyu a kauyen Ganawuri dake jihar Filato ranar Lahadi.
Wani kurtun sojan kasa ake zargin ya harbe uban gidansa da abokin aikinsa, kuma ya kashe kan shi. Za a ji kwamitin BOI zai yi bincike domin gano abin da ya faru
A wani sabon hari da aka kai jihar Kaduna, miyagun 'yan bindiga sun yi garkuwa da matar aure, 'ya'yanta biyu da wasu mazauna 9 a ƙauyen Janjala, yankin Kagarko.
Hukumar Sojin Najeriya
Samu kari