Rikici Ya Balle Tsakanin Manoma da Makiyaya a Jihar Kogi, Mutane da Dama Sun Mutu

Rikici Ya Balle Tsakanin Manoma da Makiyaya a Jihar Kogi, Mutane da Dama Sun Mutu

  • Ana fargabar mutane da dama sun mutu yayin da rikici ya ƙara balle wa tsakanin manoma da makiyaya a jihar Kogi
  • Lamarin ya faro ne tun ranar Jumu'a loƙacin da wasu makiyaya suka kashe manomi a hanyar gonarsa bayan sun masa ɓarna
  • Bayan haka ne fustattun matasa suka farmaki Fulani, suka kashe da dama kuma suka tafka ta'asar dukiya

Kogi state - Sabon rikici ya ɓalle tsakanin manoma da makiyaya a garin Isanlu, hedkwatar ƙaramar hukumar Yagba da gabas a jihar Kogi, ana fargabar mutane da yawa sun rasa rayukansu.

Jaridar Leadership ta tattaro a rahotonta cewa rikicin ya fara ne bayan wasu mahara sun mamayi manomi ɗaya a hanyarsa ta zuwa gona, sun halaka shi ranar Jumu'a.

Rikicin manoma da makiyaya a jihar Kogi.
Rikici Ya Balle Tsakanin Manoma da Makiyaya a Jihar Kogi, Mutane da Dama Sun Mutu Hoto: Alhaji Yahaya Bello
Asali: Facebook

Shugaban ƙaramar hukumar Yagba ta gabas a jihar Kogi, Honorabul Abdulrazaq Ijagbemi, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai.

Kara karanta wannan

Tsadar Rayuwa: Jami'ar Najeriya Za Ta Gwangwaje Ma'aikata Da Dalibanta Da Kayan Tallafi

Ya bayyana cewa wasu gungun fulani makiyaya ne suka farmaki manomin a hanyarsa ta zuwa gona, kuma garin haka suka yi ajalinsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban ƙaramar hukumar Yagba ta gabas ya ce:

"Manomin yana tsaka da aiki a gonarsa kwatsam wani makiyayi ya koro shanu suka shiga ciki. Bayan sun lalata masa shuka, manomin ya kama dabba ɗaya kana ya tafi kai rahoto wurin 'yan sanda."
"Jami'ai sun buƙaci ya koma ya taho da shanuwar, a hanyar zuwa gida tare da ɗan uwansa, makiyaya suka yi masa kwantan ɓauna, ɗan uwansa ya ruga ya faɗa wa mutanen gari."
"Bayan koƙarin mafarauta da mutanen gari, an samu nasarar gano gawar manomin a cikin daji bayan kwana biyu da aukuwar lamarin."

Mutane sun kai harin ɗaukar fansa

Wata majiya ta shaida wa jaridar cewa matasan garin Isanlu sun fusata da kisan manomin, bisa haka suka kai kazamin harin ɗaukar fansa kan Fulani.

Kara karanta wannan

Hawaye Sun Kwaranya Yayin Da Hayakin Janareto Ya Yi Sanadin Rasuwar Ma'aurata, 'Yayansu Da Mutane 2 a Anambra

Yayin harin ne fusatattun matasan suka kashe Fulani da yawa, wasu da dama suka jikkata. Sun kuma ƙona motar Toyota Corolla da Babura 15 duk na Fulani.

Yan Bindiga Sun Halaka Mutum 6 a Kauyukan Jihar Benuwai

A wani rahoton na daban 'Yan bindiga sun aikata mummunan ta'adi a garuruwa biyu ranar Lahadi da daddare a jihar Benuwai.

A cewar wani mazaunin yankin, yan bindigan sun shiga garin Igba Ukyor a kan Babura kuma daga zuwa suka bude wa mutane wuta kan mai uwa da wabi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel