Rundunar Sojin Najeriya Ta Ce Kin Amsa Gayyata Ta Sa Aka Kama Sojan Da Yake Wa'azi

Rundunar Sojin Najeriya Ta Ce Kin Amsa Gayyata Ta Sa Aka Kama Sojan Da Yake Wa'azi

  • Rundunar sojin Najeriya ta musanta labarin da ake yaɗawa kan wani jami'inta da ta kama
  • Rundunar ta ce ba don ya bar Musulunci ya koma Kiristanci ba ne ya sa aka kama shi
  • Ta ce an kama shi ne saboda kin amsa gayyatar da aka yi masa, da kuma guduwa da ya yi daga bakin aiki

Abuja - Rundunar sojojin Nageriya ta yi ƙarin haske dangane da wani ƙaramin Kofur, Musa Adamu, da aka kama bayan samunsa yana wa'azi a kafafen sada zumunta.

Rundunar ta ce ba wai don ganinsa da aka yi yana wa'azi a cikin kaki ba ne yasa aka kama shi ba kamar yadda The Punch ta wallafa.

Daraktan yaɗa labaran rundunar sojin, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ne ya bayyana hakan a Abuja, yayin da yake martani kan rahoton da ke cewa an kama shi ne saboda ya bar Musulunci zuwa Kiristanci.

Kara karanta wannan

Jihar Kano Na Kan Gaba a Yawan Wadanda Suka Kamu Da Cutar Mashako a Najeriya

Rundunar sojin Najeriya ta bayyana dalilin kama sojan da ya bar Musulunci ya koma Kiristanci
Rundunar sojin Najeriya ta ce kin amsa gayyata da guduwa daga aiki ne ya sa aka kama sojan da ya koma Kiristanci. Hoto: Disciple Daniel Joe Alimi
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya gudu daga bakin aiki a lokacin da aka gayyace shi

Onyema ya bayyana cewa an sami Musa yana wa'azi ne a kafar sada zumunta kuma a cikin kaki, wanda hakan ya saɓawa ƙa'idojin aikin soja a Najeriya.

Ya ƙara da cewa hakan ne ya sa aka aika masa da takardar gayyatar domin amsa tambayoyi daga manyan jami'an hukumar.

Maimakon ya amsa wannan gayyatar a cewar Onyema, sai kawai ya tsere daga bakin aiki na tsawon watanni shida, wanda hakan ya janyo hukumar ta ayyana shi matsayin wanda baya zuwa aiki ba tare da samun izini ba.

Ya kuma ce wannan matakin ya sanya jami'in kawo kansa sakamakon tsayar masa da asusun bankinsa cak da aka yi, inda daga nan ne aka damƙe shi.

Ba don ya koma Kiristanci daga Musulunci ko don yana wa'azi aka kama shi ba

Kara karanta wannan

Tallafin Tinubu: “Rabon N8,000 Duk Yaudara Ce”, Gwamnan Kaduna Ya Fadi Dalili

Birgediya Janar Onyema ya ce saɓanin jita-jitar da jama'a ke yaɗawa na cewa an kama shi ne saboda ya koma Kiristanci daga Musulunci, ya ce hakan ba gaskiya ba ne, an kama shi domin gudanar da bincike.

Ya ce kwamitin ladabtarwa na hukumar, yana bin tanadin da kundin tsarin mulkin Najeriya ya yi a kan aikin soja wanda jami'in ya saɓa da shi kamar yadda PM News ta ruwaito.

Ya ƙara da cewa, rundunar sojin Najeriya ta na da tsari na bai wa kowane ɓangare mutanen da za su riƙa gudanar da al'amuransa.

Ya bayyana cewa akwai mutanen da rundunar ta tanada a duka ɓangarorin addinai na Islama da na Kiristanci domin kula da harkokinsu.

Daga ƙarshe, Onyema ya yi kira ga 'yan Najeriya da su yi watsi da rahoton da a ke yaɗawa da ke ƙoƙarin ɓata suna da ƙimar rundunar sojin.

Sojoji sun daƙile harin kwanton ɓauna da barayin da ji suka kawo musu a Zamfara

Kara karanta wannan

"Matata Tana Zabga Mun Mari Ta Lakaɗa Mun Duka Kamar Jaki" Ɗan Kasuwa Ya Nemi Saki a Kotu

A baya Legit.ng ta kawo rahoto kan wani harin kwanton ɓauna na ɓarayin daji da sojojin Najeriya suka daƙile a jihar Zamfara.

A yayin musayar wuta, jami'an sojin Najeriya sun yi nasarar aika da dama daga cikin 'yan ta'addan zuwa barzahu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel