Jihar Niger
Gwamnan jihar Neja Mohammed Umaru Bago, ya fara tunanin hawa kan teburin sulhu da ƴan bindiga, domin magance matsalar tsaron da ta daɗe tana addabar jihar.
Mataimakin gwamnan jihar Neja, Mista Yakubu Garba, ya bayyana cewa a yanzu haka akwai mutane sama da 5,000 da ke gudun hijira a jihar sakamakon hare-haren.
Hedkwatar tsaro na kasa ta bayyana a ranar Alhamis, 17 ga watan Agusta cewa an kashe jami’an sojoji 36 a jihar Neja. Manjo Janar Edward Buba ne ya bayyana haka.
Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago ya gana da shugaban hukumar sojojin saman Najeriya kan mummunan harin da ƴan bindiga suka kai wa dakarun sojoji a jihar.
Sabon takaddama ya kunno kai a APC reshen jihar Neja inda sakataren jam'iyyar da mataimakin shugabanta suka yi murabus kwanaki bayan shugabanta ya yi murabus.
Gwamnatin jihar Neja karkashin jagorancin Mohammed Umar Bago ta ce ta fara tattaunawa da kamfanonin jirage masu zaman kansu domin fara jigilar jirage a Minna.
Akalla an kiyasta bashin da Najeriya ke bin Jamhuriyar Nijar fiye da Naira biliyan 4 na wutar lantarki kadai bayan kasar ta sayi fiye da kashi 60 na wutar.
Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umar Bago ya amsa koken kungiyar yan kabilar Ibo inda ya nada ya nada Mista George Dike a matsayin mai ba shi shawara na musamman.
Inyamurai mazauna jihar Neja sun yi kira ga Gwamna Mohammed Bago da ya nada dan kabilarsu a majalisarsa saboda gudunmawar da suke bayarwa wajen ci gaban jihar.
Jihar Niger
Samu kari