Mutum 15 cikin waɗanda aka sace a harin Islamiyyar Tegina sun gudo bayan masu tsaronsu sunyi tatil da giya

Mutum 15 cikin waɗanda aka sace a harin Islamiyyar Tegina sun gudo bayan masu tsaronsu sunyi tatil da giya

  • Mutane 15 cikin wadanda yan bindiga suka sace yayin da suka kai hari Islamiyya a Tegina sun gudo
  • Rahotanni sun ce mutanen sun bude kofar dakin da aka rufe su a daji ne sun tsere a lokacin da masu tsaronsu ke barci bayan shan giya
  • Labarin kubutar wadannan mutanen 15 ya karfafa wa mutanen Tegina gwiwa cewa sauran yaran 156 za su dawo

Wasu mutum 15 cikin wadanda yan bindiga suka sace a yayin da suka kai hari makarantar Islamiyya a Tegina, jihar Niger sun tsere daga hannun masu garkuwa a lokacin da masu tsaronsu suka yi tatil da giya, Daily Trust ta ruwaito.

Wadanda suka gudo din manya ne da aka sace tare da dalibai 156 a makarantar Islamiyya ta Salihu Tanko a cikin watan Mayu.

Hoton makarantar islamiyyar Malam Salihu da ke Tegina
Hoton makarantar islamiyyar Malam Salihu da ke Tegina. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

The Nation ta ruwaito cewa wasu majiyoyi a garin sun ce an raba mutanen da daliban sannan aka kai su wani daji da ke jihar Zamfara bayan sace su.

Yadda wadanda aka yi garkuwa da su suka tsere

Amma, an gano cewa wadanda aka sace din sun yi dabara sun bude kofar gidan da aka ajiye su a dajin a lokacin da masu tsaronsu ke sharbar barci bayan sun yi tatil da giya.

Wadanda suka tsere din sun raba kansu a dajin domin kada su sake fadawa hannun wasu masu garkuwan kamar yadda This Day ta ruwaito.

Daya daga cikin wadanda suka gudo din da ya fara isowa Tegina ya sanar da mutane abin da ya faru, hakan yasa gwamnatin jihar Niger ta fara kokarin zuwa ta taimakawa sauran wadada ake tsare da su.

An ce a halin yanzu an garzaya da shi asiti domin a duba lafiyarsa.

Daga bisani an samu rahoton cewa wasu karin mutane uku cikin wadanda aka sace din sun iso garin Tegina a safiyar ranar Lahadi, yayin da aka ceto daya daga cikinsu aka kai shi Minna inda ya ke karbar magani a halin yanzu.

Wasu daga cikin wadanda suka tsere din suna Zaria.

A halin yanzu, jami'an tsaro da mataimakin shugaban karamar hukumar Kagara sun tafi hanyar Tegina zuwa Birnin Gwari don tarbar sauran mutanen 10 da suka gudo.

Majiyar ya ce za a kawo su Minna domin likitoci su duba su.

Labarin tserewar wadannan mutum 15 din ya kafafawa mutane gwiwa cewa za a ceto sauran yaran 156.

A wani labarin daban, kun ji cewa wata daliban makarantar FGC Birnin-Yauri a jihar Kebbi wacce ta tsira daga harin a ranar Alhamis ta ce bata tunanin yan bindigan da suka kai hari makarantansu yan Nigeria ne, The Cable ta ruwaito.

A ranar, Alhamis ne yan bindiga suka kutsa makarantar a kan babura suka kuma yi awon gaba da malamai da dalibai da dama.

Yayin harin, yan sanda da ke makarantar sun yi kokarin dakile harin amma yan bindigan sun fi su yawa hakan ya yi sanadin rasuwar jami'in dan sanda.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel