Da Ɗuminsa: Yan Bindiga Sun Sace Wani Hakimi da Matansa 2 a Jihar Neja

Da Ɗuminsa: Yan Bindiga Sun Sace Wani Hakimi da Matansa 2 a Jihar Neja

- Wasu yan bindiga sun yi awon gaba da Hakimin Zungeru, Mustapha Madaki, tare da matansa guda biyu

- Rahotanni sun tabbatar da cewa maharan sun kutsa kai har cikin ɗakin matarsa sannan suka kamo shi tare da mai ɗakin

- Wannan na zuwa ne mako ɗaya da sace ɗaliban islamiyya 156 a garin Tegina duka a cikin jihar Neja

Wasu yan bindiga sun yi awon gaba da Hakimin Zungeru a jihar Neja tare da matansa biyu ranar Lahadi, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Tashin Hankali: An Tsinci Gawar Ɗaya Daga Cikin Ɗaliban Islamiyya da Yan Bindiga Suka Sace a Neja

An ɗauke Musatapha Madaki (Madakin Zungeru) tare da matan sa biyu da yammacin ranar Lahadi bayan wasu yan bindiga aƙalla 20 sun kutsa gidansa dake tsakiyar garin Zungeru.

Da Ɗuminsa: Yan Bindiga Sun Sace Wani Hakimi da Matansa 2 a Jihar Neja
Da Ɗuminsa: Yan Bindiga Sun Sace Wani Hakimi da Matansa 2 a Jihar Neja Hoto: voanews.com
Asali: UGC

Yan bindigan sun aje abun hawan su tsawon mita 500 da gidan hakimin, suka ƙarisa da kafafuwansu.

Maharan sun tafi kai tsaye zuwa gidan madakin, suka kutsa kai ɗakinsa suka fito dashi tare da matarsa ɗaya mai suna, Habiba.

KARANTA ANAN: Murna Ta Koma Ciki: Hatsari Ya Laƙume Rayukan Matasa 17 Akan Hanyar Dawowa Daga Ɗaurin Aure

Sun kuma yi awon gaba da matarsa ta biyu duk a wannan harin wanda maƙwabtan hakimin suka ce ya ɗauki kusan rabin sa'a ba tare da an kawo ɗauki ba.

Wannan na zuwa ne mako ɗaya bayan wasu yan bindiga sun kutsa cikin Islamiyyar Salihu Tanko dake Tegina, ƙaramar hukumar Rafi, inda suka sace ɗalibai 156.

Legit.ng hausa ta gano cewa tsakanin Zungeru da garin Tegina bai wuce tafiyar kilomita 30 ba kacal.

A wani labarin kuma Yan Bindiga Sun Kai Wani Mummunan Hari a Katsina, Sun Kashe Mutum 6 Tare da Jikkata Wasu da Yawa

Wasu yan bindiga kan mashin 60 sun kai hari ƙauyukan Runka da Kanawa dake ƙaramar hukumar Danmusa, jihar Katsina.

Yan bindigan sun kashe mutum shida tare da jikkata wasu da dama a mummunan harin da suka kai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262