Gwamnan Neja ya koka kan yadda 'yan bindiga suka hana karatu da noma a jiharsa

Gwamnan Neja ya koka kan yadda 'yan bindiga suka hana karatu da noma a jiharsa

  • Gwamnan jihar Neja ya koka kan yadda 'yan bindiga suka addabi jiharsa da kewayenta
  • Gwamnan ya ce 'yan bindiga sun hana yara zuwa makaranta tare da hana manoma zuwa gona
  • Ya bayyana haka ne a birnin Minna yayin kaddamar da wasu jami'an banga na musamman

Gwamna Abubakar Bello ya kaddamar da jami'an 'yan banga na musamman na jihar Neja da nufin dakile ayyukan gungun matasa mabarnata, musamman wadanda ke barna a Minna, Punch ya ruwaito.

Bello ya kaddamar da kungiyar 'yan bangan ne na musamman a Hedkwatar 'yan sanda da ke birnin Minna wadanda suka fito daga kungiyoyin tsaro daban-daban na jihar.

A cewar gwamnan, “Yayin da hukumomin tsaro ke fada da 'yan bindiga a yankunan karkara, wani sabon salo ya bullo a Minna wanda ba za a yarda da shi ba.

KU KARANTA: Mu Tagwaye Ne: Koriya Ta Arewa Na Bukatar Kara Dankon Alaka da Najeriya

'Yan bindiga sun hana zuwa karatu da noma a jihar Neja, gwamna ya koka
Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani Bello | Hoto: thisdaylive.com
Asali: UGC

"Muna da yanayi inda muke da kungiyoyin matasa da ke yakar junansu, suna haifar da rauni kan matafiya; wannan sam sam ba abin yarda bane."

Bello ya bukaci iyaye da su sauke nauyin da ke kansu ta hanyar kula da ba da tarbiya mai kyau.

"'Yan bindiga sun tilasta mana canza salon rayuwarmu a jihar Neja; sun hana yaranmu zuwa makaranta, sun hana mu tafiya a kan hanyoyinmu, sun hana manoma zuwa gona kuma a yanzu, suna kokarin hana yaranmu zuwa makarantar Islamiyya.

This Day ta ruwaito gwamnan yana bayyana kwarin gwiwar cewa, jiharsa ba za ta gaza ba, kuma zai yi mai yiwuwa wajen tabbatar da ceton al'ummarsa.

“Amma ba za a ba mu tsoro ba; ba za mu bari hakan ta faru ba. Za mu ci gaba da gudanar da rayuwarmu ta yau da kullum,” inji shi.

Kwamishinan 'yan sanda na jihar, Adamu Usman, ya ce an horar da mambobin kungiyar 'yan bangan na musamman a cikin makonni biyu da suka gabata don magance tayar da hankalin matasa a Minna.

KU KARANTA: Siyasar Kano: Jerin Wadanda Ake Kyautata Zaton Za Su Gaji Kujerar Ganduje a 2023

A wani labarin, Kungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah (MACBAN) ta nesanta kanta daga wata sanarwa da aka danganta da kungiyar, inda aka ce ta ba da wa’adin awanni 72 ga Jihar Delta don sauya dokokinta kan kiwo a sakaka, Channels Tv ta ruwaito.

A cewar Sakatare-janar na kungiyar ta MACBAN, Usman Baba-Ngelzerma, irin wannan bayanin da wasu boyayyun mutane ke yi suna yi ne kawai don haifar da rikici cikin al'umma.

Baba-Ngelzerma ya ce MACBAN amintacciyar kungiya ce da ke da fitattun mutane kamar Sarkin Musulmi a matsayin uba gareta don haka ba za ta taba yin wani abu da zai dagula zaman lafiyar kasar nan ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel