Wani Gwamnan Arewa Ya Ƙaddamar da Sabbin Jami'an Tsaro Na Musamman a Jiharsa
- Gwamnan Neja ya ƙaddamar da wasu sabbin jami'an tsaron sa kai (SVC) mutum 161 a karon farko
- Yace wannan somin taɓi ne, amma nan gaba gwamnatinsa zata ƙara ɗaukar mutane da dama
- Wannan na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin Neja wajen dawo da zaman lafiya a tsakanin al'ummar ta
A ƙokarinsa na dawo da zaman lafiya a jihar Neja, Gwamnan jihar, Abubakar Sani Bello, ya kaddamar da sabbin jami'an tsaro na musamman (SVC) da zasu gudanar da aikin su a jihar, kamar yadda vanguard ta ruwaito.
KARANTA ANAN: Kada Ku Yarda Yan Bindiga Su Kashe ku, Gwamna Ya Gargaɗi Yan Sanda
A cewar gwamnan, sabbin jami'an sa kai da ya ƙadɗamar SVC, za su yaƙi duk wasu yan ta'adda da suka hana jihar Neja zaman lafiya.
Gwamna Bello yace wannan shine karon farko, amma ya ƙara da cewa za'a sake ɗaukar wasu da dama a basu horo, sannan a tura su ƙananan hukumomin jihar.
Hakazalika, gwamnan ya damƙa sabbin motocin operation guda 20, da kuma mashina 20 ga sabbin jami'an domin gudanar da aikinsu.
KARANTA ANAN: Fulani Makiyaya Sun Kashe Mutum 2 Tare da Sace Wasu 6 a Enugu da Akwa Ibom
Rahotanni sun bayyana cewa zuwa yanzun, gwamnatin Neja ta samar da motocin Operation 89, mashin 283, Kekuna 30 da kuma keke nafef 4 ga jami'an tsaron jihar domin inganta tsaro a faɗin ƙananan hukumomi 25 dake faɗin jihar.
Daga cikin tawagar jami'an da suka amfana da irin waɗannan kayan aikin akwai, Karamin Goro, Sharan Daji, Girgizan Daji, Gama Aiki, Ayem Akpatuma I & II, Puff Adder I & II da sauran su.
A wani labarin kuma Murna Ta Koma Ciki, Yadda Jirgin Yaƙin NAF Ya Jefa Bam a Wurin Taron Ɗaura Aure a Jihar Neja
A wani harin bam da jirgin rundunar sojin sama ya gudanar a yankin garin Genu, jihar Neja, yayi sanadiyyar mutuwar wasu da suka halarci ɗaurin aure, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.
Wani shaidan gani da ido ya tabbatar da hakan, yace mazauna yankin biyu sun rasa rayuwarsu.
Asali: Legit.ng