Da Ɗumi-Ɗumi: Wani Gwamna Ya Kori Ma'aikata da Dama a Jiharsa, Ya Tilasta Wa Wasu Yin Ritaya
- Gwamnatin Neja ta bayyana cewa ta sallami ma'aikata kimanin 374 tare da tilasta wa wasu 380 yin ritaya
- Shugaban hukumar kula da ma'aikatan jihar, Alhaji Yusuf Galadima, shine ya bayyana haka ga manema labarai a Minna
- Yace gwamnati ta ɗauki sabbin ma'aikata 1,133 matasa domin cike guraben waɗanda aka kora
Gwamnatin jihar Neja ta sallami ma'aikata 374 yayin da ta tilastawa wasu ma'aikata kimanin 380 yin ritaya saboda saɓa wa dokokin jihar, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.
Hakanan kuma gwamnatin tana zargin waɗanda abun ya shafa da amfani da ranar haihuwa ta ƙarya lokacin da za'a ɗauke su aiki.
KARANTA ANAN: Ba Gudu Ba Ja da Baya a Matakin Mu Na Korar Ma'aikata, El- Rufa'i Ya Faɗawa Buhari
Gwamnatin ta yi ƙarin matakin albashi ga wasu ma'aikata kimanin 6,835 a ɓangarori daban-daban, kamar yadda punch ta ruwaito.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wani jawabi da shugaban hukumar kula da ma'aikatan jihar, Alhaji Shehu Yusuf Galadima, yayi wa manema labarai a Minna, ranar Talata.
Yace: "Hukumar mu ta duƙufa sosai wajen tankaɗe da rairaya domin tabbatar da ingantattun ma'aikata, da kwarewar su a matsayin da aka basu, da kuma sanin makamar aiki."
"A halin yanzun mun gano wasu mutum 46 da suka saɓawa dokokin da ƙa'idojin mu ta hanyar gudanar da bincike da kuma gwaji, sannan mun sallame su."
"Daga cikin su akwai likita ɗaya, da ma'aikatan fansho 31, akawuntoci 5, ma'aikatan lafiya 2 da kuma ma'aikatan ICT 4."
"Hakanan kuma, mun tilastawa wasu 380 yin ritaya saboda kama su da yin ƙarya a ranar haihuwarsu tun farkon lokacin da aka ɗauke su aiki." inji shi.
Mr. Galadima ya kara da cewa akwai wasu ma'aikata aƙalla 328 da aka sallama daga aiki bayan an shirya musu jarabawa a fannin takardun da suka gabatar lokacin da aka musu gwajin ɗaukar aiki.
Amma daga baya sai aka gano duka takardun na ƙarya ne, ba su da kwarewa a fannonin da suka gabatar.
KARANTA ANAN: Da Ɗuminsa: FG Ta Faɗi Ranar da Zata Kulle Layukan Wayar da Ba'a Haɗasu da NIN Ba
Gwamnati ta ɗauki sabbin ma'aikata na cike gurbi
Gwamnatin Neja dake da ma'aikata kusan 24,000 ta bayyana cewa ta ɗauki sabbin ma'aikata 1,133 kuma matasa domin su cike guraben da take da su.
Galadima yace: "Mun ɗauki matasa 1,133 aiki domin su cike mana gurabe a ma'aikatu, da ɓangarori daban-daban masu matuƙar muhimmanci kamar ɓangaren lafiya, ilimi da kuma hukumar kashe gobara ta jihar."
A wani labarin kuma Wani Tsohon Kwamishina Ya Sha da Ƙyar Yayin da Yan Bindiga Suka Buɗe Wa Motocinsa Wuta
Tsohon kwamishina a jihar Ondo, Joseph Ikpea, ya sha da ƙyar a hannun masu garkuwa da mutane.
Rahoto ya bayyana cewa Ikpea yana cikin bacci wasu yan bindiga suka buɗe wa tawagar motocinsa wuta.
Asali: Legit.ng