Gwamnan Neja yayi fallasa, ya bayyana yadda 'yan bindiga ke hada kai da jami'an gwamnati
- Gwamnatin jihar Neja ta kafa sabon tsarin tsaro domin duba al'muran miyagun 'yan bindiga a jihar
- Gwamnan jihar, Gwamna Abubakar Sani Bello, ya ce mulkinsa ba zai tsorata da al'amuran miyagun 'yan bindiga ba
- A cikin kwanakin nan ne 'yan bindiga suka sace dalibai 136 a makarantar Islamiyya ta Tanko Salihu dake Tegina, a jihar Neja
Gwamna Abubakar Sani Bello na jihar Neja ya zargi wasu 'yan siyasa da jami'an gwamnati da zama masu baiwa 'yan bindiga bayanai.
Leadership ta ruwaito cewa gwamnan yayi wannan zargin ne a ranar Talata, 15 ga watan Yuni yayin kaddamar da hukumar 'yan sintirin ta musamman.
KU KARANTA: Twitter tana da hannu a barnar da EndSARS tayi a Najeriya, Lai Mohammed
KU KARANTA: Faruk Yahaya: Ina da gogewa a fannin yaki, zan iya shawo kan matsalar tsaron Najeriya
Zargin hada kai da 'yan bindiga
Bello yayi ikirarin cewa wasu jami'ai yanzu su ke kaiwa 'yan bindiga bayanan siriri domin samun kudi.
Gwamnan ya ce: "Akwai 'yan siyasa da wasu masu alaka da gwamnati wadanda ke baiwa 'yan bindiga bayanan sirri. Ko taro muka yi, bayan kankanin lokaci, 'yan bindiga sai su dinga fadin abinda muka tattauna. Ban yadda da kowa ba a halin yanzu."
Ya bayyana cewa 'yan bindiga a jihar sun tirsasa jama'a sauya yanayin rayuwarsu inda suka bar komai saboda tsoro, kamar yadda The Punch ta ruwaito.
Bello ya ce: "Sun hana yara zuwa makaranta, sun hana jama'a tafiye-tafiye, sun hana manoma zuwa gonakinsu kuma yanzu suna kokarin hana yara zuwa Islamiyya."
A wani labari na daban, shugaban kasa Muhammadu Buhari zai ziyarci garin Maiduguri dake jihar Borno a ranar Alhamis na kwana daya, inji Gwamna Babagana Umara Zulum.
Gwamna Zulum ya bayyana hakan ne a yammacin ranar Talata a gidan gwamnatin jihar dake Maiduguri inda yace shugaban kasan zai duba yanayin halin da tsaron yankin arewa maso gabas yake ciki, Channels TV ta ruwaito.
A yayin ziyarar, ya ce shugaban kasan zai kaddamar da gidaje 4,000 wadanda suke daga cikin aikin gidaje na gwamnatin tarayya tare da wasu ayyukan da gwamnatin jihar ta aiwatar.
Asali: Legit.ng