Yadda Hukumar EFCC Ta Kwato Sama da N200bn cikin Shekara 1

Yadda Hukumar EFCC Ta Kwato Sama da N200bn cikin Shekara 1

  • Hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya ta samu nasarar ƙwato maƙudan kuɗi a hannun ɓarayi
  • EFCC ta ƙwato sama da N200bn a shekara ɗaya a ƙarƙashin jagorancin Ola Olukoyede wanda ya fara aiki a Oktoban 2023
  • Kakakin hukumar EFCC da ya bayyana hakan ya ce an kuma yankewa mutane 3000 hukunci waɗanda aka samu da laifi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Hukumar da ke yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC), ta kwato sama da N200bn a cikin shekara ɗaya.

EFCC ta kuma samu nasarar sanyawa kotuna su yankewa mutane kusan 3,000 hukunci a shekara ɗaya a ƙarƙashin jagorancin Ola Olukoyede.

Kara karanta wannan

Sarkin Rano ya mika bukatarsa wajen Gwamna Abba bayan an nada shi sarauta

EFCC ta kwato kudade
EFCC ta kwato sama da N200bn a cikin shekara daya Hoto: EFCC Nigeria
Asali: Facebook

Kakakin hukumar EFCC, Wilson Uwujaren ne bayyana hakan yayin wata hira da tashar Channels tv a shirinsu na 'Morning Brief' a ranar Litinin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaba Bola Tinubu ya naɗa Ola Olukoyede a matsayin shugaban hukumar EFCC a watan Oktoban 2023.

Hukumar EFCC ta samu nasarori

Wilson Uwujaren ya ce tun daga wannan lokacin hukumar EFCC ta samu nasarori a yaƙi da cin hanci da rashawa a ƙasar nan.

"Dangane da batun ƙwato kuɗi da yanke hukunci waɗanda su ne abin da manema labarai suka fi so, ya yi ƙoƙari sosai a cikin shekara ɗaya."
"Dangane da ƙwato kuɗi, mun ƙwato sama da N200bn a cikin shekara ɗaya a ƙarƙashin jagorancin Ola Olukoyede."
"A hakan babu batun kwatanta adadin kuɗin da ƙwato a Dala ko Yuro. Ƙuɗaɗen suna da matuƙar yawan gaske."

- Wilson Uwujaren

Kara karanta wannan

Badakalar N5.78bn: EFCC ta sake gurfanar da tsohon gwamna a gaban kotu

Me EFCC ta fi maida hankali a kai?

Duk da waɗannan nasarorin da aka samu, kakakin na EFCC ya ce hukumar ta mayar da hankali ne kan hana aikata laifuka maimakon yanke hukunci.

A cewarsa, akasarin hukuncin da aka yanke, an zartar da su ne kan laifukan yanar gizo ne inda matasa ke da kaso mafi yawa.

Kotu ta hana EFCC yin bincike

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (EFCC), Olanipekun Olukoyede ya nuna cewa an samu koma baya a ayyukanta.

Olanipekun Olukoyede ya ce EFCC ba za ta iya gudanar da bincike a wasu jihohi 10 na Najeriya ba, sakamakon takunkumin da kotu ta saka mata.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng