Murna Ta Koma Ciki: Yadda Jirgin Yaƙin NAF Ya Jefa Bam a Wurin Taron Ɗaura Aure a Jihar Neja

Murna Ta Koma Ciki: Yadda Jirgin Yaƙin NAF Ya Jefa Bam a Wurin Taron Ɗaura Aure a Jihar Neja

  • Jirgin yaƙin rundunar sojin sama yayi kuskuren jefa bam a kan wasu mutane dake taron murnar ɗaura aure
  • Wani shaidan gani da ido ya tabbatar da hakan, yace mazauna yankin biyu sun rasa rayuwarsu
  • Rundunar sojin sama (NAF) tace ba ta samu wani rahoto kan wannan kuskuren ba, manufarta yan bindiga ne da suka taru a yankin

A wani harin bam da jirgin rundunar sojin sama ya gudanar a yankin garin Genu, jihar Neja, yayi sanadiyyar mutuwar wasu da suka halarci ɗaurin aure, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Rahoton vanguard ya nuna cewa, an kashe yan bindiga da dama yayin wannan aiki na jirgin NAF.

KARANTA ANAN: Iyalan MKO Abiola Sun Koka Ga Shugaba Buhari, Sun Ce Har Yanzun Basu Amfama da Komai Ba

Rahotanni sun bayyana cewa harin da jirgin yaƙin ya kai ya kashe wasu makiyaya dake aikin satar shanu, kuma jirgin ya taso ne daga sansanin soji dake jihar Katsina.

Jirgin yaƙin NAF yayi kuskuren jefa bam a wurin taron ɗaura aure
Cikakken Bayani, Yadda Jirgin Yaƙin NAF Ya Jefa Bam a Wurin Taron Ɗaura Aure a Jihar Neja Hoto: vangaurdngr.com
Asali: UGC

Sai dai an gano cewa ɗaya daga cikin bam ɗin da jirgin ya jefa ya dira a wurin taron murnar ɗaurin aure a Wani Ƙauyen jihar Neja, kamar yadda wani shaidan gani da ido ya tabbatar.

Shaidan yace: "Mun hangi wani jirgi na sakin bam a maɓoyar yan bindiga, amma ɗaya daga cikin bam ɗin ya sauka a wurin taron murnar ɗaura aure a ƙauyen Argida."

"Biyu daga cikin mazauna ƙauyen sun mutu, kuma mun gano cewa wasu baƙi da aka gayyato wajen taron sun ji raunuka."

KARANTA ANAN: Maganar Sulhu Ta Ƙare, Zamu Ɗauki Matakin da Yan Bindiga Suka Fi Gane Wa, Matawalle

Amma da aka tuntuɓi kakakin rundunar sojin sama, Edward Gabkwet, yace harin bam ɗin da suka gudanar ya tafi yadda ake so cikin nasara.

Yace: "Ba a kawo mana wani rahoton cewa harin ya shafi waɗanda ba ruwan su ba, manufar mu ita ce yan bindigan dake yankin Genu. Bayan mun samu rahoton fasaha cewa sun taru a yankin suna ƙulla shirin kaiwa mutane hari."

A wani labarin kuma Gwamna Ya Bayyana Wasu Yan Siyasa Dake Samar da Motoci ga Yan Bindigan Jiharsa

Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma, ya zargi wasu yan siyasa da taimaka wa wajen rura wutar kai hari a jiharsa.

Gwamnan yayi wannan jawabi ne yayin da yake jawabin ranar demokaraɗiyya a gidan radio.

Asali: Legit.ng

Online view pixel