Da duminsa: 'Yan bindiga sun sheke likita a Magama, jihar Neja

Da duminsa: 'Yan bindiga sun sheke likita a Magama, jihar Neja

  • Miyagun 'yan bindiga sun sheke wata cikakkiyar likita mai suna Precious Chinedu a jihar Neja
  • Mazauna kauyen Salga dake karamar hukumar Magama sun ce har asibitin da take aiki suka shiga suka saceta
  • Jama'a sun kaiwa 'yan sanda da 'yan sinitiri rahoto amma washegari aka tsinci gawarta a daji makusanci

Wata cikakkiyar likita ta sheka lahira bayan wasu 'yan bindiga sun harbeta a kauyen Salka dake karamar hukumar Magama ta jihar Neja, Daily Trust ta ruwaito.

An tattaro cewa wasu miyagun 'yan bindiga ne da zasu kai su biyar suka kaiwa likitan farmaki har asibitin da take aiki.

KU KARANTA: Sojoji sun halaka 'yan ta'adda masu tarin yawa a kakkabar makonni 2 da suka yi a kudu

Da duminsa: 'Yan bindiga sun sheke likita a Magama, jihar Neja
Da duminsa: 'Yan bindiga sun sheke likita a Magama, jihar Neja. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Matasan arewa, 'yan majalisa sun bukaci daukan mataki kan barazanar sheke shugaban EFCC

Mazauna yankin sun sanar da yadda kisan ya faru

Makwabtan garin sun ce daya daga cikin makasan ya shiga asibitin kuma ya bukaci ganin likitan sannan suka tasa ta gaba zuwa wani wuri na daban.

Daya daga cikin makwabtan ya ce: "Lokacin da suka yi awon gaba da likitan, mun kai rahoto wurin 'yan sanda da 'yan sintiri. Washegari 'yan sintirin sun kira mu kan cewa sun ga gawarta a daji kuma muna zuwa muka gane likitan ce."

'Yan sandan jihar

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Neja, DSP Abiodun Wasiu bai yi tsokaci kan lamarin ba saboda har yayin rubuta wannan rahoton ba a sameshi ba.

Sai dai kuma, Ohaneze Ndigbo na jihar Neja, Chief Emmanuel Ezeugo, ya tabbatar da kisa likitan mai suna Precious Emeka Chinedu.

Ezeugo ya kara da cewa al'ummar Igbo dake yankin na cigaba da bincike kan mutuwar likitan. Yayi kira ga shugaban kasa Muhammasu Buhari da yasa hannu a cikin binciken kashe-kashen dake aukuwa a kwanakin nan.

A wani labari na daban, Sanata Ali Ndume ya ce yafi samun natsuwa da kwanciyar hankali idan yana Maiduguri, babban birnin jihar Borno fiye da idan yana garin Abuja, babban birnin kasar Najeriya, Daily Trust ta ruwaito.

Boko Haram ta dinga kai farmaki Maiduguri da garuruwan dake da kusanci da nan amma lokacin da Ndume ya zanta da Channels TV a shirin siyasarmu a yau ta ranar Alhamis, shugaban kwamitin sojin yace tsaro ya inganta a babban birnin Borno.

"Ina zama a Abuja da Maiduguri. Amma matukar ina Maiduguri, ina jin kwanciyar hankali fiye da Abuja saboda wani zai iya buga min kofa kuma ya saka min bindiga. A Maiduguri kuwa babu wannan tsoron."

Asali: Legit.ng

Online view pixel