Abun Tausayi: Iyayen Ɗaliban Islamiyya da Aka Sace a Neja Sun Fara Bin Masallatai, Coci Suna Roƙon Kuɗi

Abun Tausayi: Iyayen Ɗaliban Islamiyya da Aka Sace a Neja Sun Fara Bin Masallatai, Coci Suna Roƙon Kuɗi

  • Iyayen ɗaliban islamiyyar da aka sace a jihar Neja sun fara neman taimakon mutane domin haɗa kuɗin fansa
  • Rahotanni sun bayyana cewa iyayen yaran sun fara neman tallafi a masallatai da coci-coci
  • Shugaban makarantar ya sake magana da masu garkuwan, sun faɗa masa yaran sun fara kamuwa da rashin lafiya

Iyayen ɗaliban makarantar islamiyyar Tanko Salihu dake Tegina, jihar Neja, sun fara zuwa masallatai da majami'u suna neman tallafi domin haɗa kuɗin fansa, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Babban Dalilin da Yasa Ba Zamu Taɓa Rabuwa da Almajiranci a Arewa Ba, Ganduje

Idan zaku iya tunawa, wasu yan bindiga sun kai hari makarantar islamiyya a Neja, inda suka yi awon gaba da ɗalibai 137.

Bayan hakane maharan suka nemi a basu miliyan N200m kuɗin fansa kafin su saki ɗaliban dake hannun su.

Iyayen ɗaliban islamiyya sun shiga tashin hankali
Abun Tausayi: Iyayen Ɗaliban Islamiyya da Aka Sace Neja Sun Fara Bin Masallatai, Coci Suna Roƙon Kuɗi Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Yayin da a nata ɓangaren, gwamnatin Neja ta bayyana cewa ba zata biya kuɗin fansa domin a saki yaran ba, ta ƙara da cewa zata yi amfani da wata hanya ta daban domin kuɓutar da su.

A halin yanzun, an gano cewa iyayen yaran sun fara zuwa masallatai da coci-coci suna roƙon a taimaka musu domin su haɗa kuɗin da masu garkuwa suka nema.

Ɗaliban da Aka Sace sun fara rashin lafiya a hannun yan bindiga

Wata majiya daga garin Tegina, ta bayyana cewa maharan sun kira shugaban makarantar islamiyyar, Abubakar Alhassan, inda suka shaida masa yaran sun fara kamuwa da rashin lafiya.

Yan bindigan sun tabbatar wa shugaban cewa dukkan ɗaliban suna raye, amma wasu daga cikin su basu da lafiya saboda yana yin da suka shiga sama da makwanni biyu.

KARANTA ANAN: Karin Bayani: Yan Majalisar Wakilai Sun Tantance Sabon Hafsan Soji, Manjo Janar Farouk Yahaya

Abubakar ya tabbatar da cewa ya sake tattaunawa da yan bindigan kuma sun rage kuɗin fansan zuwa miliyan N150m.

Yace: "Ban jima da yin magana da yan bindigan ba, kuma sun tabbatar mun duka ɗaliban mu suna nan a raye. Amma ba zaka ƙi tsammanin cewa basu da lafiya ba, saboda yanayin da suka tsinci kansu a ciki."

A wani labarin kuma Wani Gwamnan Arewa Ya Ƙaddamar da Sabbin Jami'an Tsaro Na Musamman a Jiharsa

Gwamnan Neja ya ƙaddamar da wasu sabbin jami'an tsaron sa kai (SVC) mutum 161 a karon farko, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Yace wannan somin taɓi ne, amma nan gaba gwamnatinsa zata ƙara ɗaukar mutane da dama.

Asali: Legit.ng

Online view pixel