Musulmai
Mai alfarma Sarkin Musulmai, Sa'ad Abubakar III, ya ce ba zasu yi shiru ba har sai an yi wa al'ummar da harin jirgin sojoji ya shafa a kauyen Tudun Biri adalci.
Jarumar fina-finan Nollywood, Mercy Aigbe ta bayyana dalilin Musuluntarta inda ta ce shaukin soyayya ce ta kwashe ta bayan ta cire rai a samun kwanciyar hankali.
Gwamnan Kaduna, Malam Uba Sani, ya ɗauki alkawarin cewa ba zai runtsa ba a koƙarin tabbatar da an yu wa waɗanda harin bam a ya shafa a Tudun Biri adalci.
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ce gwamnatinsa za ta hukunta duk wanda aka gano yana da hannu a tashin bama-bamai a kauyen Tudun Biri da ke jihar Kaduna.
Mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya sauka a filin jirgin sansanin sojin sama da ke Mando domin zuwa ta'aziyya kan harin bama-baman soji.
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya yu ta'aziyyar mutanen da suka mutu a harin bam din da sojoji suka kai kan masu bikin Maulidi a Kaduna.
Kungiyar nan mai fafutukar kare hakkin Musulmai MURIC ta buƙaci Gwamnatin tarayya ta gudanar da bincike mai tsafka kan abin da ya jawo kisan masu maulidi a Kaduna.
Sanatan Kaduna ta kudu, Sunday Marshall Katung, ya ce zai haɗa kai da sauran yan majalisar tarayya na jihar domin kwato hakkin mutanen da aka kashe a Tudun Biri.
Wata baturiya mai shekaru sittin da biyu ta samu nasarar yin saukar Al-Kur'ani a wata makarantar islamiyya a Kano. Shekarunta talatin kenan a jihar Kano.
Musulmai
Samu kari