"Dole a yi adalci" Sarkin Musulmi Ya Maida Zazzafan Martani Kan Jefa Wa Musulmi Bam a Kaduna

"Dole a yi adalci" Sarkin Musulmi Ya Maida Zazzafan Martani Kan Jefa Wa Musulmi Bam a Kaduna

  • Sultan Sa'ad Abubakar na III ya buƙaci mahukunta su yi wa musulman da harin bama-baman soji ya shafa a kauyen Tudun Biri
  • Sarkin Musulmi a Najeriya ya ce ba zasu yi ƙasa a guiwa ba, zasu ci gaba da matsa lamba har sai mutanen sun samu adalci
  • Babban hafsan tsaron ƙasa, Janar Christopher Musa, ya bayyana lamarin da babban abun takaici da nadama

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kaduna - Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III, ya buƙaci mahukunta su yi adalci ga waɗanda harin bama-baman soji ya shafa a kauyen Tudun Biri.

Mai alfarma sarkin Musulmai, Alhaji Sa'ad Abubakar.
"Ba zamu haƙura ba" Sarkin Musulmi Ya Maida Zazzafan Martani Kan Jefa Wa Musulmi Bam a Kaduna Hoto: Daular Usmaniyya
Asali: Facebook

Sama da mutane 120 ne suka rasa rayukansu sakamakon jefa bam har sau biyu da jirgin sojojin kasa ya yi a taron Maulidi a kauyen da ke ƙaramar hukumar Igabi, jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Gwamna Uba Sani ya ɗauki wasu muhimman matakai masu kyau kan jefa wa Musulmi bam a Tudun Biri

Sarkin Musulmin ya nemi a yi wa mutanen adalci ne yayin da yake jawabi a wurin bikin cikar Sarkin Jema'a na 11, Muhammad Isa Muhammad (CON), wasu shekaru a karagar mulki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zamu tabbatar an yi adalci - Sultan

Daily Trust ta tattaro cewa yayin da yake jawabi a fadar Sarkin da ke Kafanchan, Sultan ya ce ba zasu haƙura ba, zasu ci gaba da matsa lamba har sai an yi adalci kan lamarin.

"Ba mun zo nan taya Sarki murna kaɗai bane, mun zo ne mu yi wa masarauta addu'a tare da rayukan bayin Allah da aka kashe a jihar Kaduna."

"Zamu ci gaba matsa lamba kan wannan lamari har sai mun ga an yi wa mutanen da ibtila'in ya shafa adalci," in ji Sultan.

Babban hafsan soji ya maida martani

Da yake martani, babban hafsan hafsoshin sojin kasa, Janar Christopher Musa ya bayyana abin da ya faru a Kaduna a matsayin abin takaici da nadama.

Kara karanta wannan

Kaduna: Gwamna Sani ya caccaki kalaman DHQ kan dalilin jefa bam a taron Musulmai, ya nemi abu 1

A rahoton The Nation, Musa ya ce:

“Nauyin da ke kanmu shi ne mu kare rayukan ’yan kasa, za mu dauki kwakkwaran mataki don ganin irin wannan abu bai sake faruwa a ko’ina a kasar nan ba."
"Shugaban ƙasa ya ba da umarnin gudanar da bincike mai zurfi kan abin da jawo yin wannan kuskuren," in ji shi.

Uba Sani Sani ya ɗauki alkawari kan harin Tudun Biri

A wani rahoton kuma Malam Uba Sani ya ce gwamnatin Kaduna zata yi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da adalci ga al'ummar kauyen Tudun Biri.

Gwamnan ya ce zai bi diddigin binciken da za a yi har zuwa ƙarshe domin tabbatar da an hukunta masu laifi a harin bam ɗin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262