Rikicin Kungiyar Izala Ya yi Sanadiyyar Tafiya Kotu, An Rufe Masallaci Na Shekaru 7

Rikicin Kungiyar Izala Ya yi Sanadiyyar Tafiya Kotu, An Rufe Masallaci Na Shekaru 7

  • Rigimar da ke tsakanin ‘Yan Jama'atul Izalatul Bid'ah wa Iqamatus Sunnah ya fito fili a karamar hukumar Moriki
  • Akwai masallacin da aka rufe na tsawon shekara da shekaru a dalilin rigimar bangaren Jos da ‘yan Kaduna
  • Rikici a game da wanda zai yi limanci ya haddasa fitina, yanzu ba a salloli, karatu da sauran ibada a masallacin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Zamfara - Jama'atul Izalatul Bid'ah wa Iqamatus Sunnah ta yi karin haske a game da abin da ya jawo rufe masallaci a Moriki.

A wani jawabi da kungiyar ta fitar a shafin Facebook a ranar Alhamis, an fahimci rigimar kungiyar ya yi dalilin daina salloli.

Izala
Masallacin Izala a Moriki Hoto: Jibwis Live Radio, Maradi haske, Jibwis
Asali: Facebook

'Yan Izala sun je kotu a kan masallaci

Kara karanta wannan

"Zamani ya canza" Shugaban JAMB ya faɗa wa ɗalibai yadda zasu samu aiki bayan gama digiri a Najeriya

Kungiyar ta ce ba ta so yin magana a game da zancen ba domin an kai maganar kotu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta tabbatar da cewa kungiyar Izala ta reshen Kaduna mallaki wannan sanannen masallaci Juma’a da ke garin Moriki.

Tun ba yau kungiyar ta mallaki fili kuma ta gina wannan masallaci da jama’a su ke amfani da shi wajen ibada a jihar Zamfara.

Silar rigimar 'Yan Izala a Moriki

Da mataimakin limamin ya rasu, sai aka ga cewa akwai bukatar a samu wani madadinsa wanda zai rika jagorantar sallar jama’a.

Ganin an sasanta tsakanin bangaren Jos da na Kaduna a lokacin, sai aka dauko sabon limami daga bangaren ‘yan Izalar Jos.

A sakamakon mutuwar wannan limami, sai aka nemi wani daga bangaren Kaduna ya hau kujerarsa ganin su ke da masallacin.

Wannan mataki da aka dauka ne ya haddasa sabani tsakanin bangarorin inda ‘yan reshen Jos su ka ce dole su za a ba limanci.

Kara karanta wannan

"Ainahin dalilin da yasa muka tsige gwamna da yan majalisar PDP 16": Alkalin kotun daukaka kara

Kungiyoyin Izala a kotu

Bayanin ya ce an je kotun shari’a amma an gagara samun mafita, dole aka tafi gaban wani alkali da ke garin Kauran Namoda.

Sanarwar ta ce kotu ta yi watsi da karar da lauyan bangaren Izalar Jos ya shigar.

Wani mutumi, Hanafi Musa Turakin Moriki ya nemi ya ginawa ‘yan bangaren Jos wani masallacin, amma su ka nuna ba su bukata.

Da Abdul'aziz Yari yake gwamna, ya nemi a ginawa bangaren Jos wani masallacin, amma shi ma bai yi nasara ba, har yanzu ana kotu.

Malamai su nemi diyya a Tudun Biri

Malaman musulunci da dattawan Arewa sun nemi diyya daga hannun gwamnati a kan wadanda aka kashe a garin Tudun Biri.

Sojoji sun yi kuskuren jefa bama da ya kashe mutane wajen maulidi, malaman Izala da na dariku duk sun soki abin da ya faru.

Asali: Legit.ng

Online view pixel