Masu Garkuwa Da Mutane
Dakarun yan sanda da haɗin guiwar mafarauta sun yi nasarar sheke masu garkuwa 3 yayin da suka yi yunkurin sace wasu mutum biyu a jihar Adamawa jiya Laraba.
Wani DPO na ‘yan sanda ya ki amincewa da karbar cin hancin naira miliyan daya da wani dan bindiga ya ba shi bayan an kama shi a wani otal da ke garin Kaduna.
Jami'an sashin yaƙi da garkuwa da mutane na rundunar yan sandan Abuja sun samu nasarar ceto mutane 14 da aka yi garkuwa da su, sun sheƙe mutum ɗaya.
Gawurtaccen mai garkuwa da mutane a birnin tarayya Abuja, ya musanta ƙaifin da yan sanda suke tuhumarsa da shi. Ya ce shi dan fanshi da makami ne.
Wasu gwamnoni akalla 9 a Najeriya sun tabbatar da aniyarsu ta zartar da hukuncin kisa ko ɗaurin rai da rai kan duk wanda aka kama da laifin garkuwa da mutane.
Rundunar 'yan sanda ta kama Mansir Hassan, wanda ke yi wa 'yan ta'adda safarar makamai a dajin Zurmi, jihar Zamfara. An kama shi ne a yankin Zariya a kan babur.
Yan sanda sun kama mata da miji da suka yi karyar an yi garkuwa da su don su samu kudin fansa har naira miliyan biyar da nufin sayen gida a Badagry da ke Legas.
Gwamnatin jihar Anambra ta ce ta gano wani ramin karkashin kasa wanda masu garkuwa ke ajiye wadanda suka sace a ciki, a wani yunkurin gwamnati na dawo da tsaro.
Shehu Sani ya tabbatar da sakin tsohon shugaban wata makaranta a Kaduna a ranar Talata, 23 ga watan Janairu. An tsare shi a lokacin da ya je kai kudin fansa.
Masu Garkuwa Da Mutane
Samu kari