Gwamna Abba, Sule da Wasu Gwamnoni 7 da Suka Shirya Zartar da Hukuncin Kisa Kan Masu Garkuwa

Gwamna Abba, Sule da Wasu Gwamnoni 7 da Suka Shirya Zartar da Hukuncin Kisa Kan Masu Garkuwa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Lamarin garkuwa da mutane na ci gaba da ƙaruwa a Najeriya cikin ƴan watannin nan yayin da hukumomin tsaro ke kokarin magance duk wani kalubalen tsaro a ƙasar.

Jaridar Punch ta tattaro cewa akalla jihohi 10 sun sha alwashin fara yanke hukuncin kisa ko ɗaurin rai-da-rai kan duk wanda aka kama da laifin satar mutane.

Abdullahi Sule, Abba Kabir da Soludo.
Cikakken Jeri: Sunayen Gwamnoni 10 Da suka shirya yanke hukuncin kisa kan masu garkuwa Hoto: Abba Kabir Yusuf, Abdullahi Sule, Charles Soludo
Asali: Twitter

Legit Hausa ta haɗa muku jerin gwamnonin jihohin da suka yi wannan yunƙuri, ga su kamar haka:

Abba Kabir Yusuf na Kano

Ta bakin Sanusi Tofa, daraktan midiya da yaɗa labarai, Gwamna Yusuf ya ce gwamnatinsa zata fara aiwatar da dokar yaƙi da masu garkuwa da mutane.

Kara karanta wannan

Kano: An aike da babban saƙo ga Gwamna Abba kan kwamishinan da ya yi wa alƙalai barazanar kisa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dokar dai ta tanadi hukuncin kisa ga duk wanda aka kama da hannu a aikata laifin satar mutane a Kano.

Tofa ya ce:

"Zamu ci gaba da aiwatar da hukuncin kisa kan masu garkuwa da mutane kamar yadda tsohuwar gwamnatin da ta gabata ta kafa doka."

Hyacinth Alia na Benuwai

Gwamna Alia ta bakin Antoni Janar kuma kwamishinan shari'a na jihar Benuwai, ya ce gwamnatinsa ta shirya aiwatar da dokar yaki da garkuwa, wadda ta tanadi hukuncin kisa.

Kwamishinan ya bayyana cewa a halin yanzun gwamnatin ta gurfanar da mutane da dama da ake zargi da aikata laifin garkuwa da mutane a gaban kotu.

Douye Diri na Bayelsa

Jihar Bayelsa mai arzikin man fetur tana da dokar yaƙi da garkuwa da mutane wanda ta baiwa gwamna damar rattaba hannu kan hukuncin kashe duk mai hannu a satar jama'a.

Kara karanta wannan

EFCC za ta gurfanar da tsohon gwamna kan wani laifin da ya aikata lokacin yana ofis

Tsohon gwamnan jihar, Seriake Dickson ne ya zartar da dokar bayan majalisar dokoki ta amince da ita. Wata majiya ta ce gwamnatin Diri ba zata sauya dokar ba.

Charles Soludo na Anambra

Wani jami'i a ma'aikatar shari'a ta jihar Anambra ya ce majalisar dokokin jihar ta yi wa dokar manyan laifuka garambawul.

A cewarsa, majalisar ta maida garkuwa da mutane ya zama laifin da za a yanke wa duk wanda aka kama da aikatawa hukuncin kisa.

Ya ce:

"A yanzu dokar ta ce laifi ne da za a yanke hukuncin kisa kan duk wanda aka kama da aikata garkuwa da mutane, wataƙila a ɗan yi gyara ta yadda za a sa hukuncin ɗaurin rai-da-rai."

Abdullahi Sule na Nasarawa

A 2020, Gwamna Sule ya rattaba hannu kan dokar garkuwa da mutane wadda ta tanadi hukuncin kisa kan duk wanda aka kama da laifin, sannan gwamnati zata kwace dukiyarsa.

Haka nan gwamnati zata kwace duk wata kadara da aka yi amfani da ita wajen aikata garkuwa, kuma mai wannan kadarar zai zaman gidan yari na shekara 20.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Plateau ta sanya dokar hana fita na tsawon awanni 24, bayanai sun fito

Sauran jihohin da suka shirya aiwatar da dokar yaƙi da masu garkuwa da mutane sun haɗa da gwamnonin Enugu, Kwara, Ondo da kuma gwamnan Osun.

Magoya bayan NNPP da APC sun yi arangama

A wani rahoton kuma Rundunar ƴan sandan Kano ta ce ta shirya gurfanar da waɗanda ta kama da aikata laifuka daban-daban bayan hukuncin kotun ƙoli.

Rahoto ya nuna yan sanda sun ayyana wani Habibu a matsayin wanda suke nema ruwa a jallo kan rikicin siyasar da ya faru a Gaya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel